Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, kara yin nazari kan muhimman fannoni, tushe ne na cimma burin raya kimiyya da fasaha mai inganci, kana hanya ce ta raya kasa mai karfin kimiyya da fasaha a duniya. David Gross wanda ya samu lambar yabo ta Nobel a fannin Physics ya nuna amincewa ga wannan ra’ayi yayin da yake hira da wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG a kwanakin baya, inda ya ce, kasar Sin tana kokarin kasancewa wata kasa mai wadata da karfi, ya kamata Sin ta taka rawar kan gaba a fannin kimiyya da fasaha, shi ya nuna yabo ga kokarin kasar Sin.
Malam Gross ya yi nuni da cewa, duk lokacin da ya zo kasar Sin, sai ya ji ban mamaki sosai, ya ga babban canji kan gine-gine da ayyukan more rayuwa, har ma a fannin kimiyya da fasaha, da ba da ilmin jami’a, da kuma karuwar dalibai masu begen yin nazarin kimiyya da fasaha. A fannin da malam Gross ya yi nazari, Sin ta riga ta samu wasu muhimman nasarori, ta kera mabudin hangen nesa mai lakabin “FAST” mafi girma a duniya, wannan ya burge duniya sosai. (Zainab Zhang)