Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya yi kira da jama’ar jugar da su kara bayar da ta su gudunmawar don ganin an kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar.
Gwamnan, a sakonsa na sabuwar shekara a ranar Litinin, ya ce gwamnatinsu ta dukufa wajen ganin ta shawo kan matsalar tsaro da sauran kalubalen da ke addabar jihar.
- Gwamna Radda Ya Yi Allah Wadai Da Hare-haren ‘Yan Fashin Daji A Jihar Katsina
- Ba Zan yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba, Cewar Dikko Radda
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Ibrahim Kaula-Mohammed, ya fitar, ya bukaci al’ummar jihar da su hada kai, su kulla alaka mai karfi da juna, da niyyar tunkarar kalubalen jihar.
Ya gode wa jama’a bisa hadin kai da goyon bayan da ya samu na kafa kungiyar sa ido ta jama’ar Katsina, wadda aka kafa domin magance matsalar rashin tsaro a jihar.
Radda ya ba da tabbacin cewa “gwamnati tare da jama’a, za su magance matsalar rashin tsaro.”
Ya kuma bayyana yadda gwamnatinsa ta himmatu wajen samar da hadin kai da bunkasar tattalin arziki da da kawo ci gaba.
Gwamnan ya shawarci jama’ar jihar da su yi amfani da damar da ake da ita don rage zaman kashe wando da talauci da dora jihar kan turbar da ta dace.
Ya bayyana fatansa cewa jihar za ta kasance mai girma da wadata a shekarar 2024.
Radda ya bukaci jama’a da kada su yi watsi da goyon bayan da suke bai wa gwamnati yayin da take kokarin magance kalubalen da jihar ke fuskanta.