• English
  • Business News
Friday, August 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Burin Sin Na Kara Jin Dadin Zaman Jama’a Ya Dace Da Begen Jama’ar Kasa Da Kasa

by CGTN Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Burin Sin Na Kara Jin Dadin Zaman Jama’a Ya Dace Da Begen Jama’ar Kasa Da Kasa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shekarar da ta gabata, shekara ce da bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya farfado, bayan ta kyautata matakan dakile da kandagarkin cutar COVID-19, wadanda ta dauki shekaru 3 tana gudanar da su. Ko da yake an fuskanci matsaloli da dama, amma dukkan Sinawa sun yi kokari don ba da gudummawarsu.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fada a cikin jawabinsa na murnar sabuwar shekarar 2024, wato “Muna da babban burin da muke fatan cimmawa, burin da ke shafar kowa, wato za mu yi kokarin ganin al’ummar Sinawa na kara jin dadin zaman rayuwarsu”. Kara jin dadin zaman rayuwa shi ne babban burin kasar Sin, kana ya dace da begen jama’ar duniya baki daya.

  • Shugabannin Sin Da Rasha Sun Tura Wa Juna Sakwanni Don Murnar Sabuwar Shekara
  • Xi Da Biden Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 45 Da Kulla Huldar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu

Idan ana son jama’ar duniya su kara jin dadin zaman rayuwa, da farko ana bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kasar Sin ta yi kokari wajen gabatar da ra’ayinta kan daidaita rikicin Ukraine ta hanyar siyasa, da takardar daidaita rikicin dake tsakanin Palesdinu da Isra’ila, da tura jami’ai da dama don shiga tsakani kan daidaita rikicin, wanda ya samu amincewa daga kasa da kasa.

Bunkasuwa shi ne mabudin daidaita dukkan matsaloli. A cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, tattalin arzikin Sin ya karu da kashi 5.2 cikin 100 a rubu’i uku na farkon shekarar 2023 bisa na makamancin lokacin shekarar 2022, Sin ta kiyaye matsayinta na kasa mafi bayar da gudummawa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Kana Sin ta kafa dandalin hadin gwiwa da dama don more damar samun bunkasuwa tare da kasashen duniya.

Jama’a a fadin duniya suna rayuwa mai kyau, kuma suna fatan samun karin adalci a harkokin duniya. An gudanar da taron kolin Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, da dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya karo na uku, da shigar da sabbin membobi a cikin BRICS, da ganawa a tsakanin shugabannin Sin da Amurka a San Francisco, kasar Sin ta yi kokarin kiyaye tsarin kasa da kasa, da raya karfin kasashe masu tasowa, da kuma ba da tabbaci da kwanciyar hankali ga duniyar dake fuskantar sauye-sauye da rikici.

Labarai Masu Nasaba

Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12

Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

A yayin da aka shiga sabuwar shekara, ba ma kawai Sin tana tunanin kanta kadai ba, har ma da duniya baki daya. A shekarar 2024, kasar Sin tana son hada kai da kasashen duniya wajen tinkarar kalubale da sa kaimi ga samun wadata tare. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 'Yan siyasar AmurkaAlakar sin da AmurkaSin
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ta’addanci: NDLEA Ta Cafke Miyagun Kwayoyi Zuwa Dazukan Zamfara Da Kebbi

Next Post

Za Mu Cigaba Da Fadakarwa Kan Dorewar  Zaman Lafiya Tsakanin Arewa Da Kudu – Sarkin Kano

Related

Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12
Daga Birnin Sin

Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12

3 hours ago
Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan
Daga Birnin Sin

Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

4 hours ago
Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji
Daga Birnin Sin

Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji

4 hours ago
Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza

6 hours ago
Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama

7 hours ago
An Bude Gasar Wasannin Ta Duniya Ta 2025 A Chengdu
Daga Birnin Sin

An Bude Gasar Wasannin Ta Duniya Ta 2025 A Chengdu

8 hours ago
Next Post
Sarkin Kano

Za Mu Cigaba Da Fadakarwa Kan Dorewar  Zaman Lafiya Tsakanin Arewa Da Kudu – Sarkin Kano

LABARAI MASU NASABA

Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar 

Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar 

August 7, 2025
Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12

Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12

August 7, 2025
Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

August 7, 2025
Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan

August 7, 2025
Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji

Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji

August 7, 2025
Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas 

August 7, 2025
Neja

Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago

August 7, 2025
Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza

Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza

August 7, 2025
Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana

Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana

August 7, 2025
Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama

Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama

August 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.