Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce zai ci gaba da fadakarwa tare da inganta ayyukan da za su samar da zaman lafiya tsakanin yankin Arewa da Kudu maso Gabas da ma daukacin yankunan kasar nan domin tabbatar da dorewar Nijeriya a matsayin kasa daya.
Sarki Bayero ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar a wajen kaddamar da shirin samar da zaman lafiya a Kudu-maso-Gabas (PISE-P) a karamar hukumar Bende ta jihar Abia.
- Murnar Sabuwar Shekara: Gwamna Kefas Ya Yi Wa Fursunoni 31 Afwa A Taraba
- Tudun Biri: Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Kwamitin Sa Ido Kan Rabon Gudunmawa
Shirin wanda mataimakin kakakin majalisar wakilai Rt. Hon. Benjamin Okezie Kalu ya shirya, an yi shi ne domin neman hanyar da ta dace don magance matsalolin tsaro a yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya.
Sarkin ya yi kira ga mataimakin shugaban majalisar da ya yi amfani da wannan shiri wajen taimakawa talakawa da marasa galihu da ke yankin, inda ya ce, hakan zai taimaka wajen rage musu kalubalen tattalin arziki.
Ya kuma yi kira da a kara yin addu’o’in Allah ya dawwamar da hadin kai da zaman lafiya a tsakanin ‘yan Nijeriya baki daya.