Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce, ta ceto rayuka 417 da dukiyoyi da kudinsu ya kai kimanin Naira biliyan 1.2 a wasu gobara da aka samu a jihar daga watan Janairu zuwa Disamba, 2023.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN a ranar Talata a Kano, inda ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa kan kashe gobara 659 a cikin shekarar.
- Matatar Dangote Ta Karbi Danyen Mai Karo Na 4 Daga NNPC
- Hare-Hare: Gwamnatin Filato Ta Ayyana Zaman Makokin Mako Guda
Ya kara da cewa, mutane 100 ne suka rasa rayukansu a cikin wannan lokaci yayin da aka yi asarar dukiyoyi sama da Naira miliyan 451 sakamakon tashin gobara a sassa daban-daban da ke fadin jihar.
Abdullahi ya dora alhakin tashin gobarar akan sakaci da iskar gas din girki, amfani da na’urorin lantarki marasa inganci, da adana man fetur a gidaje da wuraren da ba su cancanta ba da dai sauransu.
Ya shawarci daukacin mazauna garin da su yi taka tsantsan da abubuwan da ke saurin kamawa da wuta da sauran abubuwan da ka iya haifar da tashin gobara.