Gwamnatin tarayya ta dakatar da karatun digiri daga jami’o’in jamhuriyar Cotonou da Togo.
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ce ta sanar da hakan bayan wani bincike na sirri da wata kafar jarida ta yanar gizo a Nijeriya ta yi wanda ya fallasa badakalar da dalibai da jami’o’in ke tafkawa wajen mallakawa daliban takardar shaidar kammala digiri.
Rahoton binciken ya nuna cewa, wani dan jarida ya samu digiri a Jami’ar Cotonou a cikin makonni shida kuma ya shiga cikin shirin hidimtawa kasa na shekara guda da hukumar NYSC ke gudanarwa.
Ga jerin sunayen jami’o’in kasashen waje da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta haramta kararu acikinsu, kamar yadda hukumar NUC ta bayyana a shafinta na yanar gizo:
1. Jami’ar Kimiyya da Gudanarwa, Port Novo, Jamhuriyar Benin, da sauran cibiyoyinta a Nijeriya.
2. Jami’ar Volta, da ke Ghana, da sauran cibiyoyinta a Nijeriya.
3. International University, Missouri, USA, Kano da Lagos, da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
4. Jami’ar Collumbus, UK, tana aik.da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
5. Tiu International University, UK, da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
6. Jami’ar Pebbles, UK, da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
7. London External Studies UK, da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
8. Pilgrims University da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
9. Jami’ar Kirista ta Yammacin Afirka, da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
10. EC-Council University, USA, Ikeja Lagos Study Centre.
11. Concept College (London), Ilorin, da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
12. Jami’ar Houdegbe ta Arewacin Amurka da ke Nijeriya.
13. Makarantar Kasuwanci ta Jami’ar Irish a London, da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
14. Jami’ar Ilimi, Winneba, Ghana, da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
15. Jami’ar Cape Coast, Ghana, da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
16. African University Cooperative Development, Cotonou, da duk wasu cibiyoyinta a Nijeriya.
17. Jami’ar Yammacin Pacific, Denver, Colorado, da ke da Cibiya a Owerri.
18. Jami’ar Evangel ta Amurka da Chudick Management Academic, Legas.