‘Yansanda a Morocco sun kwace tan 1.488 na hodar iblis a wani samamen hadin gwiwa da jami’an tsaron Spaniya.
An gano hodar iblis din ne boye cikin kwalayen ayaba da aka makara su cikin kwantenar kaya ta jirgin ruwa da ya taho daga Kudancin Amurka zuwa Turkiyya.
An yi kamen ne a tashar jirgin ruwa ta Tanger Med a Arewacin Morocco.
Mahukuntan Moroccon sun ce suna zargin an shigo da hodar iblis din ne a wani yunkuri na safarar miyagun kwayoyin zuwa kasashen duniya amma har yanzu suna gudanar da bincike.
Lamarin ya faru ne kwana daya bayan mahukunta sun kwace hodar iblis mai nauyin kilo 363 daga wata babbar mota da ke kokarin shiga Morocco ta iyakar kasar da Mauritania.
An gano cewa kasar da ke Arewacin Afrika ita ce babbar hanyar da ake amfani da ita wajen safarar miyagun kwayoyi daga Kudancin Amurka zuwa Turai.