Kafar sadarwa ta TGnews, ta karrama gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, tsohon gwamnan jihar Umaru Jibrilla Bindow, da wasu mutum 18, ranar Asabar.
Kafar ta kuma karrama tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, da Admiral Jamila Sadiq Malafa (mai ritaya), da dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Song/Fufore a majalisar wakilai ta kasa Honorabul Aliyu Wakili Boya.
- Gobara Ta Lalata Shaguna 10 A Adamawa
- Isra’ila Na Kara Iza Wutar Rikici A Sassan Gabas Ta Tsakiya -Lebanon
Haka kuma kafar ta karrama mataimakin shugaban jami’ar tarayya da ke Kashere Jihar Gombe, Farfesa Umar Pate, Reberan Dakta Panti Filibus, LCCN. Arch Bishop, Sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu, sarkin Ganye Gangwari Ganye, Alhaji Adamu Sanda, Hama Bachama Homun Ismaila Daniel Shaga da Kwandi Nunguriya, Mai Martaba Kuruhaye Dishon Dansanda.
Sauran mutanen da kafar ta karrama su ne shugaban bangaren labarai na kafar sadarwar talabijin na TVC, Stella Din-Peters, Mal Hamisu Idris Medugu, Barista Shafari Shadrach Kanya, tsohon dan majalisar dokokin jihar Honarabul Hassan Mamman Barguma, Ardo Usman da Madam Celina Yakubu.
Da yake jawabi lokacin karbar lambar yabon, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya gode wa kafar sadarwar yada labarai ta TGNews, bisa yadda ya amince da kokarin gwamnatinsa na ganin an samar da shugabanci na gari ga jama’a.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakiyarsa Farfesa Kaletapwa Farauta, ya yi alkawarin ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya ga ’yan jihar, tare da gode wa wadanda su ka shirya taron bisa karramawar da aka masa.
Da shi ma ke jawabi a bikin mataimakin shugaban jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya dake Kashere, Farfesa Umar Pate, ya ce fasahar sadarwa ta kawo sauyi ba kawai a fannin aikin jarida ba, har ma a rayuwar dan adam baki daya.
Farfesa Pate ya yaba wa kamfanin dillancin labarai na TG game da shirya taron kuma ya bukaci ‘yan jarida da su rungumi gagarumin sauyin da fasahar sadarwa ta kawo, tare da baiwa jama’a bayanai da rahotanni na gaskiya.
A jawabinsa na maraba, Babban Edita/Mawallafin TG News, Tom Garba, ya yaba wa wadanda su ka samu kyautar da kuma wadanda su ka dauki lokaci na halartan taron, tare da nuna godiyarsa ga bikin karramawar da ya bayyana da “mai dimbin tarihi”
Haka kuma kafar TGNews, ta kaddamar da mujalla ta farko ta TGNews Magazine, da za ta rika fita wata-wata domin ci gaba da hidimta wa al’umma.