Wani babban jami’in Dandalin Tattauna Tattalin Arzikin Duniya (WEF) Chen Liming, ya ce rawar da kasarsa ke takawa kan manyan batutuwan da suka shafi makomar bil adama, abu ne mai matukar muhimmanci da ake matukar bukata.
Yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Chen Liming ya ce a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki, kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a fannoni kamar na siyasar duniya da tattalin arziki da kirkire-kirkiren fasahohi.
- Sin Ta Mayar Da Martani Kan Yadda Amurka Ta Sayar Wa Taiwan Makamai
- Yawan Masu Bude Ido Da Suka Ziyarci Yankin Xizang Ta Sin Ya Kai Sabon Matsayi A Shekarar 2023
Ya ce tsarin tafiyar da harkokin duniya na fuskantar sauye-sauye, inda Sin ke kara taka rawar gani wajen inganta tsarin.
Har ila yau, ya ce asusun bada lamuni na duniya IMF ya kara hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Sin a shekarar 2024, haka zalika an kaddamar da dabarun inganta tattalin arzikin bangarori masu zaman kansu da karfafawa baki zuba jari, bisa imanin cewa kasar Sin za ta ci gaba da zama jagora wajen farfado da tattalin arzkin kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)