Biyo bayan karuwar rashin tabbas a hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma hare-haren masu garkuwa da mutane, babban sufeton ‘yansandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya kaddamar da shirin matakan inganta tsaro a kan hanyar.Â
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Muyiwa Adejobi ne, ya bayyana hakan a ranar Alhamis.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Kauyen Katsina
- Ramadan: Gwamnatin Tarayya Ta Yunkura Kan Shawo Kan Hauhawar Farashin Sukari
Ya ce “Lura da yadda abubuwa suke wakana da kuma yadda muke samun bayanan sirri dole ne za mu kara kaimi tare da daukar matakai masu tsari kan ganin an magance wannan matsalar, ciki kuwa har da kara yawan jami’an tsaron da suke kan hanyar” in ji mukaddashin matamakin Sufeton mai lura da bangaren ayyukan na musamman Ede Ayuba Ekpeji.
Ya kuma bukaci jama’a da su sanya ido, su kai rahoton duk wani abu da ake zargi, tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro.
Ya kuma tabbatarwa da jama’a cewa wadannan tsauraran matakan tsaro wani bangare ne na ci gaba da kokarin tabbatar da yanayi mai tsaro da kwanciyar hankali.