Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya nada sabbin shugabannin bankunan Nijeriya uku wadanda aka rushe shugabanninsu a ranar Laraba.
A wata sanarwa da ya fitar da yammacin Laraba, Hakama Sidi Alli, mukaddashin daraktan yada labarai na CBN, ya bayyana Yetunde Oni a matsayin sabon manajan darakta da shugaban bankin Union da Mannir Ubale Ringim a matsayin babban darakta.
- A Kara Yawan Jami’an Tsaro A Hanyar Abuja- Kaduna – Sufeton ‘Yansanda
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Kauyen Katsina
Bankin ya sanar da Hassan Imam, a matsayin wanda zai rike mukamin babban darakta kuma babban jami’in bankin Keystone.
Chioma A. Mang za ta yi aiki a matsayin babban darakta a bankin.
Sanarwar kuma ta sanar da manajojin da za su jagoranci bankin Polaris, inda Lawal Mudathir da Omokayode Akintola a matsayin manyan manajojin gudanarwa da kuma Chris Onyeka Ofikulu a matsayin babban darakta.
Sanarwar ta ce manajojin za su kama aiki nan take ba tare da bata lokaci ba.