Zargin badakalar kudi a Ma’aikatar Jin Kai ta Tarayya ta fiye da Naira Biliyan 44.5 ta mamaye kafafen yada labarai a wannan makon musamman bayan dakatar da ministar ma’aikatar, Dakta Betta Edu da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a kan badakalar Naira Miliyan 585 daga cikin biliyoyin da ake zargi a kai tare da bayar da umarnin Hukumar Yaki da Zamba da Karya Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) ta bincike ta.
Har ila yau, duk dai a makon nan ne tsohuwar ministar ma’aikatar, Sadiya Farouk, ta amsa gayyatar EFCC bisa binciken wasu makudan kudi sama da Naira Biliyan 37.
- Minista Sadiya Ta Mika Ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinkai Ga Babban Sakatare
- EFCC Ta Ƙwace Gidaje 40 Da Wasu Wurare Mallakar Sanata Ekweremedu
Tuni dai (EFCC) ta fara gudanar da binciken ministocin biyu kari a kan wanda take yi tsohuwar shugabar Hukumar Kula da Da Jin Dadin Al’umma (NSIP), Halima Shehu ita ma saboda zargin badakalar wasu makudan kudade da aka ce ‘wai’ sun kai Naira biliyan 44, lamarin da Halimar ta musanta.
Matakin da Shugaba Tinubu ya dauka na dakatar da Minista Edu ya samu yabo da jinjina ga ‘Yan Nijeriya da dama saboda yadda labarin zai tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro a kan cin hanci da rashawa a tsakanin jami’an gwamnati.
Wata majiya ta bayyana mana cewa, shugaban kasa ya yi amfani ne da shawarar da EFCC ta bayar a kan dakatar da Edu don a samu cikakkiyar damar binciken ta yadda ya kamata. “binciken ba zai gudana yadda ake so ba matukar tana kan kujerarta, “a kan haka muka nemi, a kawar da ita don gudanar da bincike kamar yadda shugaban kasa ya umarta” in ji majiyar.
Jim kadan bayan sanar da dakatar da ita, Edu ta garzaya fadar shugaban kasa (Aso Billa) don ganawa da shi, amma hakarta ba ta cimma ruwa ba. Majiyarmu a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafar sada zumunta, an ga dakatacciyar ministar tana barin fadar shugaban kasa bayan da aka hana ta ganin Shugaba Tinubu a wata mota daban bayan da aka janye motocinta na alfarma tare da masu yi mata hidima.
Ana zargin Dr. Betta Edu da rubuta takardar neman Babbar Akanta ta Kasa Mrs. Oluwatoyin Sakirat Madein ta amince mata ta biya wata mai suna Bridget Mojisola Oniyelu Naira 585,189,500.00 a asusun bankinta, wanda hakan ya saba wa dokokin kudi na gwamnatin tarayya. Tuni dai Akanta Janar ta nesanta kanta da batun.
Wannann badakalar na zuwa ce cikin wattanin da shigowar gwamnatin Tinubu wanda cikin yakin neman zabenta ta yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa.
Shugabannin jami’iyun ‘yan adawa sun nemai a gudanar da ciakken bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a badakalar.
Haka kuma, a nata bangaren, tsohuwar Ministar Ma’aikatar ta Jin Kai, Sadiya Umar-Farouk, wadda take ci gaba da zuwa EFCC don amsa tambayoyi yayin rubuta wannan rahoton, ana zarginta ce da badakalar Naira 37,170,855,753.44 ta hanyar amfani da wani dan kwangila mai suna James Okwete.
Ana zargin Sadiya Farouk ta wawure wadanna kudaden ne a lokacin da take jagorantar ma’aikatar a zamanin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kamar yadda binciken farko ya nuna.
Tun da farko sai da tsohuwar ministar ta bayar da hakuri a kan rashin amsa gayyatar EFCC a ranar da suka nemi ganin ta da farko. Jami’in yada labarai na hukumar EFCC Dele Oyewale ya tabbatar da cewa, tsohuwar Ministar Sadiya Farouk ta rubuta takardar bayar da hakuri kan hakan. Kana ya tabbatar da cewa a halin yanzua tana ba jami’an hukumar dukkan hadin kan da ake bukata.
Badakala ta uku da ake zargi a ma’aikatar ita ce ta tsohuwar Shugabar Hukumar Kula da Da Jin Dadin Al’umma (NSIP), Halima Shehu wadda Shugaba Tinubu da ya dakatar da ita har sai an gudanar da bincike kan zargin da ake yi mata na karkatar da Naira biliyan 44. Masu bibiyar dambarwar sun yi imanin cewa, badakalar da ake zargin Halima Sheshu ce, ta tono sauran badakalolin da ake bincike a Ma’aikatar ta Jin Kai.
…Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba – Atiku
A martaninsa, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna takaicinsa a kan yadda gwamnatin APC a karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu take wasa da shirin yaki da fatara a kasar nan, ya kuma lura da cewa, dakatar da ministar jin kai Dr Betta Edu a bin a yaba ne duk da cewa har yanzu da sauran rina a kaba.
Atiku ya bayyana haka ne a takardar sanarwa da jam’in watsa labaransa, Phrank Shaibu ya raba wa manema labarai a Abuja.
“Duk da cewa Tinubu ya cancanci a yaba masa kan dakatar da Edu, amma mun yi imanin cewa wannan mataki ne da ya kamata a dauka tuntuni.
“Da farko, ba shi da wata hujja ta nada ta a matsayin minista a ma’aikatar da ke da muhimmanci irin wannan tun da farko. Tinubu ya sanya siyasa a gaban cancanta, don haka wannan badakala ta faru.
“Wace gogewa ce Betta ta samu a fannin aiki? Yaya aka yi watsi da Imaan Ibrahim, duk da tarin gogewarta?
“Yaya shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya tsaya a matsayin wakilin Betta Edu a lokacin da ake tantance ta a majalisar dattawa?
“A gaskiya, ba Betta Edu kadai ke da hannu a cikin wannan badakala ba. Rahotanni sun nuna cewa wasu a cikin gwamnatin Tinubu sun samu kudi daga wannan ma’aikatar a karkashin wata kungiya mai suna ‘Renewed Hope Initiatibe’.”
“Bai kamata Betta Edu ta zama ita kadai a wannan badakala ba. Wadanda suka kudaden da aka tanadar wa talakawan Nijeriya ya kamata a kama su, a bincike su kuma a gurfanar da su a gaban kuliya. Shedanci da mugun hali a yi sata da sunan talakawa.” In ji sanarwar.
…Martanin Jam’iyyar APC
Hakazalika, da take mayar da martini, jam’iyyar APC ta bayyana dalilin da ya sa Shugaba Tinubu ya dakatar da Ministar Jin Kai Betta Edu Jami’iyyar a matsayin matakin da ya dace kana ta ce, lallai hakan yana nuna jajircewarsa a kan yaki da rashawa da gwamnatin APC ke jagoranta.
Jami’in watsa labarai na jami’iyyar na kasa, Felid Morka, ya bayyan haka a tattauanwarsa da gidan talabijjn na Channels, ya kuma ce, dole duk wani jami’in gwamnnati da ya aikata ba daidai ba ya dandana kudarsa.
…A Fadada Binciken Zuwa Sauran Ma’aikatu – Kungiyoyin Fararen Hula
Kungiyoyi da masu rajin kare hakokkin bil’adam da dama sun yaba da matakan da shugaban kasa ya dauka a kan dambarwar, musamman yadda ya dauki matakin dakatar da Ministar Jin Kai Dr. Betta Edu ba tare da bata lokaci ba.
A tsokacinsa, shugaban kungiyar CSCHEI, Kunle Yusuff, ya ce, kungiyoyi masu zaman kansu ba za su amince da cin amana ba daga wadanda shugaban kasa ya nada su jagoranci wata ma’aikata.
Haka kuma, shugaban kungiyar matasan Arewa (AYCF), Alhaji Yerima Shettima, ya ce, Shugaba Tinubu ya yi daidai a matakin da ya dauka na dakatar da wadannan jami’ai da ake zargi da wasoson dukiyar al’umma.
Ana kara samun yawaitar masu kiraye kireyen a fadada wannan binciken zuwa wasu ma’aikatun gamnatin tarayya musamman ganin yadda sunayen wasu manyan jami’an gwamnati ke kara fitowa a cikin wannan badakalar ta ma’aikatar Jin Kai irin su Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.
…Mata 8 Da Badakalar Kudi Ta Dabaibaiye Su ‘Yan Shekarun Nan
Yawanci a kan siffanta mata da rikon amana fiye da maza, musamman a game da abin da ya danganci sha’anin kudi. Hakan ya sa hatta a kungiyoyi ake yawan nada mata a mukamin ma’aji da sakataren kudi da sauransu, haka ma a gwamnati.
Amma a baya-bayan nan, zargin badakalar kudi da sauransu ya rika kunno kai a ofisohin wasu fitattun mata da ke rike ko suka taba rike manyan mukaman gwamnatin Nijeriya.
Wasu daga cikinsu zargin ne yayi sanadin rabuwarsu da kujerunsu, wasu kuma bayan sun kammala wa’adinsu ne suka fuskanci bincike.
Ga wasu shahararru daga cikinsu:
Patricia Etteh: Tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilai daga watan Yuli zuwa Oktoba, 2007, Patrici Ette ta rasa kujerarta a sakamakon badakalar kudade da aka bankado a kasafin kudin majalisar. Haka nan EFCC ta zarge ta da karbar cin hanci daga wani kamfanin samar da makamashin hasken rana da aka ba wa kwangila a Jihar Akwa Ibom da ke shiyyar kudu maso kudu, na kimanin Naira Miliyan 130.
Stella Oduah: Zargin facaka da kuma karkatar da makudan kudade musamman sayo motoci masu sulke na daruruwan miliyoyi sun dabaibaye tsohuwar ministar sufurin jiragen sama a zamanin shugaba Goodluck Jonathan, zargin da aka jima ana kai-komo tsakanin Stella Oduah da kuma hukumar EFCC.
Diezani Alison-Madueke: Tana fuskntar shari’a a kan bddadakalar da aka shafe sama da shekaru 10 ana fafatawa a tsakaninta da EFCC bisa zargin wawure biliyoyin kudade da suka kai Dala Biliyan 2.5. Diezani ta tsere zuwa kasar Birtaniya amma ba ta tsira ba, domin an gurfanar da ita a can a gaban shari’a.
Pauline Tallen: Bayan zargin tsohuwar ministar harkokin mata, Paulin Tallen da karkatar da Naira biliyan biyu, kotu ta haramta mata rike mukamin gwamnati har sai ta janye kalamantan gami da ba ba da hakuri kan kiran hukuncin kotun da ta soke nasarar Aisha Dahiru Binani a zaben takarar gwamnan Jihar Adamawa a karkashin APC a matsayin hukuncin je-ka-na-yi-ka.
Muheeba Dankaka: Zargin badakalar karbar miliyoyin kudade daga hannun masu neman aiki a Hukumar Raba Daidai ta kasa da ke karkashin shugabancinta. Muheeba dai ta musanta zargin har ta yi rantsuwa a gaban kwamitin majalisar dokoki kasa cewa ba ta da hannu a ciki.
Halima Shehu: An dakatar da Shugabar Hukumar ba da tallafin dogaro da kai (NSIP), kan tura kudaden gwamnati kimanin biliyan 44 zuwa asusun wasu mutane da hukumomi ba bisa ka’ida ba. Halima dai ta ce ta yi haka ne sakamakon umarni da matsin lamba daga ministar jin kai Bette Edu, amma ita tun da farko ba ta gamsu da hakan ba.
Sadiya Umar-Farouk: Ana zargin ta da karkatar da Naira biliyan 37 ta hannun wani dan kwangila, amma ta musanta sanin dan kwangilar ballantana mu’amala da shi.
Betta Edu: Bakalalar kudaden tallafin talakawa daga hukumar kula da shirin, da kuma neman amfani da ofishin Akanta-Janar na Kasa wajen karkatar da Naira miliyan 583 na tallafin jihohi hudu zuwa asusun wata mata.