Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya jagoranci tallafin tara kudi ga iyayen ‘yan mata shida da aka yi garkuwa da su kwanan nan a gidansu da ke Unguwar Bwari a Abuja, domin ceto sauran ‘ya’yansu mata daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, masu garkuwa da mmutanen, sun kashe Nabeeha Al-Kadriyar daliba mai matakin digiri (400, Biological Science) da ke Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya a Jihar Kaduna a ranar Juma’a, yayin da kuma wasu ‘yan uwanta guda biyar – Najeebah da ke matakin digiri (500 Level, Quantity Survey) da Nadheerah da ke matakin digiri (300 Level, Zoology), da sauran ukun da har yanzun ke hannun masu garkuwar, inda suke neman kudin fansa har Naira Miliyan N60m.
Da yake magana a shafinsa na X (Twitter) a ranar Lahadi, Pantami, wanda malamin addinin Musulunci ne, ya ce, duk da cewa, ba ya goyon bayan biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane amma tun da har sun kashe Nabeeha, sun kuma yi barazana ga rayukan sauran wadanda ke tsare a wurinsu, hakan ya tilasta dole a nemi mafitar ceto sauran.
Tsohon ministan ya ce, ya yi magana da wani abokinsa, wanda ya ba da gudummawar kudi har Naira miliyan 50 don ceto sauran da ke tsare a wurinsu.