Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wani dan ta’adda da ake nema ruwa a jallo daga cikin wadanda suka tsere daga gidan yarin Kuje biyo byan harin da ‘yan ta’adda suka kai na balle gidan yarin a ranar Tatalar makon jiya a Abuja.
A cewar sanarwar manema labarai da daraktan yada labarai na NDLEA, Femi Babafemi ya fitar, ya ce dan ta’addan da ake zargi da tserewa mai suna Suleiman Sidi, an cafke shi ne da safiyar ranar Litinin a garejin motoci da ke Area 1 a cikin Abuja sa’ilin da ke kokarin shiga motar kabu-kabu domin guduwa zuwa garin Maiduguri ta jihar Borno.
Sanarwar ta ce, an gano sinki-sinki na tabar wiwi guda uku a tare da wanda aka kaman wato Suleiman Sidi.
Sanarwar na cewa, “Tambayoyin farko-farko da aka yi masa, dan ta’addan da ake nema ruwa a jallon ya tabbatar da cewa shi din yana tsare ne a gidan yarin Kuje bisa zargin ta’addanci da fashi da makami, ya kuma kara da cewa, shi din yana daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin a ranar Talatar da ta gabata.”
Sanarwar ta kara da cewa, shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai murabus) ya umarci a mika dan ta’addan da aka kaman ga hukumar kula da gidajen yarin kasa (NCoS).
Kazalika, shugaban ya jinjina tare da yaba wa irin kokarin jami’ansu na cikin birnin tarayya Abuja bisa cafke dan ta’addan da suka yi.