A ko da yaushe kasashen yamma na tsarguwa kan sakamakon huldar Sin da Afirka. Masana suna da yakinin cewa, bayan duka mummunan zarge-zarge da hannunka mai sanda da kasashen yamma ke ci gaba da yi kan alakar Sin da Afirka ta hanyar ikirarin cewa, kasar Sin ta dana ma kasashen Afirka “tarkon basussuka”, kasashen yamma sun tsinci kansu a cikin takaici saboda kara ingantuwar alaka tsakanin Sin da Afirka.
Kasancewar ministocin harkokin wajen kasar Sin sun kiyaye al’adar ziyartar Afirka tun daga shekarar 1991, a cikin lokuta masu kyau da ma marasa kyau, na nuni da yadda bangarorin biyu ke mutunta alakar dake tsakaninsu. A tsakiyar shekarar 2023, alal misali, Wang Yi ministan harkokin wajen kasar Sin, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya ziyarci Afirka ta Kudu, Najeriya, Kenya da Habasha kan batutuwa da dama da suka hada da BRICS, da kayayyakin more rayuwa da kuma yafe basussuka. Kuma ministan ya fara ziyarar farko na 2024 a nahiyar daga ranar 13 zuwa 18 ga watan Janairu, inda zai ziyarci kasashen Masar, Tunisia, Togo da Cote d’Ivoire. Daga nan zai zarce zuwa Brazil da Jamaica, kasashe biyu dake da tarihin al’adun Afirka.
- Ofishin Kula Da Harkokin Taiwan Na Majalisar Gudanarwa Da Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Sun Yi Tsokaci Kan Sakamakon Zabukan Taiwan
- Yadda Aikin Gine-gine Na Kasar Sin Suka Taimaka Wajen Gudanar Da Gasar Cin Kofin Afirka
Dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta kara karfi, yayin da bangarorin biyu ke ci gaba da hadin gwiwa a matakai daban daban, ba wai kawai a fannin tattalin arziki da diflomasiyya ba. A matsayinsu na kasa da nahiya masu tasowa mafi girma, bangarorin biyu suna da kamanceceniya ta fuskar hangen nesa da kalubalen da ya kamata su shawo kansu a bangarori daban-daban, har ma da matakin siyasa.
Domin daidaita hadin gwiwar dake tsakaninsu, bangarorin biyu sun kaddamar da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC) a shekarar 2000. Dandalin mai wakilai 55 ya kunshi kasar Sin, da kasashen Afirka 53 da ke huldar diflomasiyya da kasar Sin, da kuma Hukumar Tarayyar Afirka. Taron manyan jami’ai karo na 16 na FOCAC da aka gudanar a nan birnin Beijing a watan Oktoban da ya gabata, ya jaddada aniyar bangarorin na samun moriyar juna, da samun ci gaba tare da hadin gwiwar samun nasarori tare. A shekarar 2021, kungiyar ta aiwatar da sama da kashi 70 cikin dari na sakamakon taron kolin FOCAC na Beijing a shekarar 2018.
Dangantakar Sin da Afirka ta kara karfi a lokacin da cutar numfashi ta COVID-19 ta barke. Kasar Sin ta ba da gudummawar kayayyakin jinya da suka hada da kayan aiki, magunguna, ma’aikata da alluran rigakafi na miliyoyin daloli don taimakawa nahiyar ta yaki cutar. Ita ma Afirka ta ba da gudummawa ga yakin da kasar Sin ke yi da cutar ta hanyar ba da goyon baya ta dabi’a da biyayya a farkon annobar. Hakan dai ya faru ne a daidai lokacin da kasashen yamma ke kyamatar kasar Sin tare da neman mayar da kasar Sin saniyar ware. Bayan COVID-19, kasar Sin ta ci gaba da tallafawa tattalin arzikin Afirka ta hanyar inganta harkokin cinikayya da samar da ababen more rayuwa ga nahiyar.
Bisa kididdigar da hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar a watan Agustan shekarar 2023, cinikayya tsakanin Sin da Afirka ya karu da kashi 7.4 cikin dari a duk shekara zuwa kusan dala biliyan 158.36 a rubu’i biyu na farkon shekarar. Kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayyar Afirka cikin shekaru goma da suka gabata.