An rantsar da Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo a karo na biyu a ranar Litinin.
Uzodimma ya yi rantsuwar ne da misalin karfe 3:23 na rana, don ci gaba da jan ragamar jihar a wa’adi na biyu.
- Tinubu Ya Naɗa Ministan Yada Labarai Cikin Kwamitin Yi Wa Shirin Tallafi Garambawul
- Yadda Mota Ta Buge Mai Kwacen Waya A Kano
Rantsuwar wadda aka yi ta a filin wasa na Dan Anyiam Owerri, da ke babban birnin jihar, ta samu halarta manya tare da jiga-jigan mutane daga ciki da wajen jihar.
Talla
An kuma rantsar da Lady Chinyere Ekomaru a matsayin mataimakiyar gwamnan jihar Imo.
Taron dai ya samu sa albarka shugaban kasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, muk’arraban gwamnati da kuma ‘yan jami’iyyar APC.
Talla