A jiya Talata, Jafaru Yakubu, shugaban kwamitin huldar dake tsakanin kasashen Najeriya da Sin a karkashin majalisar wakilai ta kasar Najeriya, ya gabatar da wata sanarwa kan sakamakon “zaben” da aka yi a yankin Taiwan na kasar Sin, inda ya jaddada matsayin kasar Najeriya na goyon bayan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.
Sanarwar ta ce, “zaben” da ya gudana a yankin Taiwan na kasar Sin, da yadda wasu mutane ke neman “’yancin kai” na yankin, ba ma kawai sun sabawa babbar manufar kasar Najeriya game da huldarta da kasar Sin ba, har ma sun keta ikon mulkin kai na kasar Sin.
Jafaru Yakubu ya ce, kasar Najeriya ta sake nanata matsayinta na bin manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Ta san Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, wanda ba wanda zai iya balle shi, kana gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin halastacciyar gwamnati ce daya tak dake wakiltar daukacin kasar ta Sin. Najeriya ta ki amincewa da duk wani mataki na balle yankin Taiwan daga kasar Sin, da na tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe, kana kasar ta nuna cikakken goyon baya ga kasar Sin bisa burinta na dinke dukkan yankunanta waje guda ta hanyar lumana. (Bello Wang)