Hukumar kashe gobara ta jihar Bauchi, ta ce ta ceto rayukan mutane 310 sakamakon ibtila’in gobara 393 da aka samu a fadin jihar a shekarar 2023 da ta gabata.
Mohammed Bature, jami’in hulda da jama’a na hukumar ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN a ranar Alhamis a Bauchi.
- NIN-SIM: Masu Hulda Da Kamfanonin Sadarwa Sun Koka Kan Katse Layinsu Daga Tsarin Kira
- Za A Rataye Mutane 2 Sakamakon Kashe Dan Acaba A Adamawa
Mohammed ya ce, “Gobara ta lalata dukiyoyi da kiyasinsu ya kai Naira miliyan 137, an kums samu asarar rayukan mutane shida.
“A cikin shekarar 2023 hukumar ta samu kiraye-kirayen tashin gobara 293, kiraye-kirayen ceto rai 49 da kuma kiraye-kiraye 17 kan rugujewar gingine-gine.
“Mafi yawancin tashin gobarar na faruwa ne sakamakon rashin kula da amfani da iskar gas na girki da kuma amfani da na’urorin lantarki marasa inganci.”
Mohammed ya kuma kara jan hankulan al’umma, inda yace “Ya kamata mutane su yi taka tsantsan kan yin amfani da iskar gas wurin girki, ya kuma da ce, a tabbatar an kashe kayan lantarki lokacin da ba a amfani da su”
Kakakin ya kara da cewa Gwamna Bala Mohammed ya samar da karin motocin kashe gobara guda hudu domin kara aikin hukumar wajen magance matsalar gobara a jihar.