• English
  • Business News
Friday, August 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Abba Kabir Yusuf: Kano Na Bukatar Sabuwar Alkibla

by Farfesa Faruk Sarkinfada
2 years ago
in Bakon Marubuci
0
Gwamna Abba Kabir Yusuf: Kano Na Bukatar Sabuwar Alkibla
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata

Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari

Bayan nasarar da Allah Madaukakin Sarki ya bai wa Gwamnan Jihar Kano Eng Abba Kabir Yusuf a kotun koli ta Nijeriya bisa tabbatar da zaben sa, Jihar Kano na bukatar sabuwar alkiblar jagoranci da ta gaza samu tun dawowar mulkin demokradiyya a shekarar 1999.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na bukatar assasawa da gudanar da jagorancin da zai tabbatar da zaman lafiya da ci gaba da bunkasar arzikin Jihar Kano ta hanyar dinke baraka ta bangarori da dama, musamman na siyasa, malamai da masarautu, don samun nasarar gudanar da mulkin adalci ga jama’ar Jihar Kano. Mai girma Gwamna ya na da kyakyawan abin koyi daga rayuwar fiyayyen halitta, Annabin mu Muhammadu tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, dangane da kalubalen da ya fuskanta a karon farko, da kuma daga bisani yayin da budi da nasarar Ubangiji Allah su ka saukar masa.

  • ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Satar Keke-napep A Kano
  • Jihar Kaduna Za Ta Ƙarfafa Ƙawancen Tattalin Arziki Da Ƙasar Jamus

A karon farko, yayin halin tsanani da jarrrabawa na tsawon shekaru goma sha uku a garin Makka, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rayu cikin kyawawan dabi’u, kamar dogaro ga Allah, juriya, rashin tsoro, hakuri, da su ka bayyana yayin halin gwagwarmaya wadanda ba za a iya fahimtarsu ba a cikin halin yalwa da iko.  Ya kuma ci gaba da isar da sako ba tare da gajiyawa ba duk da rashin yawan mabiya da kuma tsangwama da ya yi ta fuskanta.  Wannan juriya da tsaiwa tsayin daka a kan kira ga Allah ya ja hankulan da yawa daga cikin wadanda ba su ba da gaskiya ba suka musulunta. A kashi na biyu na rayuwarsa, wato lokacin da nasara ta samu, iko da mulki suka samu Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya bayyana kyawawan halaye kamar su hangen nesa, yafiya, kauna, saukin kai, da jajircewa, wadanda su ka kara jawo hankulan mutane da dama ya zuwa musulunci.  Ya yafe wa wadanda suka nuna masa tsana da kiyayya, ya ba da cikakken tsaro da kariya ga wadanda suka fitar da shi daga mahaifarsa (Makka), ya ba da dukiya mai yawa ga matalautansu.  Wadannan kyawawan dabi’u ya sa ko da wadanda ke adawa su ka karbi kiran Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma duk tsirarun makiyansa suke zama masu kaunarsa daga bisani.

Hakika mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf na da kyakyawan darussa daga rayuwar Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata gare shi a halin tsanani da ya shiga tun zaben 2019, sanda bai sami nasarar zama Gwamnan Kano ba, da kuma halin nasarar sa a yanzu da ya yi nasara a zaben 2023 kuma kotun koli ta Nijeriya ta tabbatar masa da wannan Nasara. Gwamna Abba Kabir Yusuf na bukatar dinke baraka a wannan lokaci, ta hanyar yafiya, musamman ga wadanda su ka tsangwame shi a baya da kuma kyakyawan hangen nesa, nuna kauna, saukin kai, da jajircewa, da kare hakkin duk wani mai hakki ba tare da nuna bambanci ta kowannen bangare ba.

Jinjina ga mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf don kafa Majalisar Dattawan Kano (KEC), wadda za ta zama mai ba da shawara ga gwamnati, kuma ta hada da muhimman jagorori ‘yan asalin Jihar Kano, da kuma tshofaffin gwamnonin ta, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, Malam Ibrahim Shekarau da Kuma Dr Abdullahi Umar Ganduje.  Har wa yau, mu na kira da babban murya musamman ga wadannan shuwagabanni uku da su ka mulki jama’ar Kano tun daga 1999 zuwa yanzu, su kau da banbance-banbancen da ke tsakanin su wajen tallafa wa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf don samar wa Jihar Kano sabuwar alkiblar shugabanci na gari. Hakika a tsawon shekaru kusan 24, kowanne daga cikikin wadannan shuwagabanni ya ba da gudunmawa, gwargwadon ikon su, wajen samar da ayyukan ci gaba ta bangarori da dama a Jihar Kano. A yanzu ne mutanen Kano su ka fi bukatara gudunmawarku wajen wanzar da abubuwan alkhairai da ku ka dasa, da kuma cike gurabun da ku ka bari, don bunkasar Jihar Kano a Nijeriya da duniya gaba daya.  Hakika za su zamanto ababen alfahari a gare mu in har wannan tsari ya tabbata.

Shi fa kyakyawan shugabanci mai dorewa, ya na samuwa ne lokacin da aka samu jagororin da su ka cancanta daga cikin al’uma, kuma ma su zartar da kudurorin da su ka dace a lokutan da su ka dace, domin tunkara da warware matsalolin da ke addabar al’umar su a wannan lokaci. Lallai Kanawa na matukar kishirwar ingantaccen shugabanci tare da hadin guiwar dukkanin masu ruwa da tsaki daga shuwagabannin siyasa, malamai, sarakuna, ‘yan kasuwa, ma’aikata, ma su manya da kananan sana’o’i da matasa da dukkanin jama’a. Don haka dole ne a rage, ko a kawar da banbance-banbancen siyasa da kiyayya a tsakanin shuwagabanni da mabiya a wannan jiha tamu, domin mu tunkari manyan matsalolin mu na cin hanci da rashawa, magudin zabe, matsanancin talauci, tabarbarewar ilimi, lafiya da tattalin arziki da kuma siyasar rashin kishin talaka ta hanyar yawan ketarawar daga jam’iyya zuwa wata jam’iyyar don maslahar kawunan su.

Kano na bukatar sabuwar alkibla don wanzar da matsayin ta na cibiyar kasuwanci da al’adu da siyasar Arewacin Nijeriya. Allah Madaukakin Sarki ya shiryar da shuwagabannin mu, Ya ba mu lafiya da zaman lafiya da yalwar arziki mai amfani, amin.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Zaɓen Sule A Matsayin Gwamnan Nasarawa

Next Post

Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Nasir Idris A Matsayin Gwamnan Jihar Kebbi

Related

Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata
Bakon Marubuci

Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata

26 minutes ago
Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari
Bakon Marubuci

Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari

1 month ago
Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus
Bakon Marubuci

Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus

1 month ago
Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 
Bakon Marubuci

Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 

2 months ago
SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)
Bakon Marubuci

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)

2 months ago
SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (2)
Bakon Marubuci

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (2)

3 months ago
Next Post
2024: Gwamnan Kebbi Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Yi Wa Kasa Addu’a Da Marawa Tinubu Baya

Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Nasir Idris A Matsayin Gwamnan Jihar Kebbi

LABARAI MASU NASABA

Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata

Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata

August 15, 2025
Shugaba Tinubu Ya NaÉ—a Sabon Darakta-Janar Na NTA Da Wasu Daraktoci

Shugaba Tinubu Ya NaÉ—a Sabon Darakta-Janar Na NTA Da Wasu Daraktoci

August 15, 2025
Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda

Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda

August 15, 2025
Bayan Gargadi Daga Gwamnatin Tarayya: Jihohin Arewa 15 Sun Fara Daukar Matakan Dakile Ambaliyar Ruwa

Bayan Gargadi Daga Gwamnatin Tarayya: Jihohin Arewa 15 Sun Fara Daukar Matakan Dakile Ambaliyar Ruwa

August 15, 2025
Matsalar Shugabanci A Jihohi Ke Haifar Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki Ga Yara

Matsalar Shugabanci A Jihohi Ke Haifar Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki Ga Yara

August 15, 2025
Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare

Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare

August 14, 2025
NLC Ta Baiwa Gwamnati Kwanaki 7 Don Magance Badaƙalar Satar Kuɗin Ma’aikata

NLC Ta Baiwa Gwamnati Kwanaki 7 Don Magance Badaƙalar Satar Kuɗin Ma’aikata

August 14, 2025
Sashen Aikewa Da Kunshin Sakwanni Na Sin Ya Bunkasa Cikin Watanni 7 Na Farkon Bana

Sashen Aikewa Da Kunshin Sakwanni Na Sin Ya Bunkasa Cikin Watanni 7 Na Farkon Bana

August 14, 2025
Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Kaduna Ta Yi Watsi Da Kalaman El-rufa’i Akan Zargin Maguɗin Zaɓe

Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Kaduna Ta Yi Watsi Da Kalaman El-rufa’i Akan Zargin Maguɗin Zaɓe

August 14, 2025
Salon Zamanantarwa Na Sin Kyakkyawan Misali Ne Ga Kasashen Afirka

Salon Zamanantarwa Na Sin Kyakkyawan Misali Ne Ga Kasashen Afirka

August 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.