A yayin da muke shiga sabuwar shekara 2024, harkokin kasuwanci na fuskantar manyan matsaloli da barazanar da za su bayar da gudummamwar durkusherwar su da hana su walwala.
Shugaban kungiyar masu masana’antu ta kasa, (MAN), Segun Ajayi-Kadir, ya yi hasashen cewa, shekarar 2024 za ta zo da manyan kalubale ga masu masana’antu saboda alamu sun nuna babu kyakyawar fata musamman a cikin watanni 6 na farkon shekarar.
- Jihar Kaduna Za Ta Ƙarfafa Ƙawancen Tattalin Arziki Da Ƙasar Jamus
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Satar Keke-napep A Kano
Nazari ya nuna cewa, matsalolin za su addabi kanana da manyan masana’natu wadanda za su taso daga harkokin tattalin arziki na ciki da wajen Nijeriya.
Musamman ma kungiyar MAN ta bayyana cewa, za a samu nakasu a bunkasar masana’antu daga kashi 2.4 a shekarar 2021 zuwa kashi 0.48 a zango na uku na shekarar 2023.
Ana iya ganin irin wannan ci bayan a manyan kamfanonin kasashe irin su Chana da Amurka, Nijeriya kuma ba za ta iya kare kanta daga wadannan abubuwan ba.
Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa, matsalolin cikin gida kama daga karyewar darajar Naira da tashin kudin ruwa suna kawo cikas ga bunkasar kamfanonin kasuwanci da kashi 50 a cikin dai.
Za kuma a iya tuna manyan kamfanoni 6 da suka fice daga Nijeriya a cikin wata shida da suka wuce, wadanda suka hada da kamfanin samar da abinci na ‘Procter & Gamble’, Unileber, GladoSmithKline Consumer Nigeria Plc, Sanofi, French pharmaceutical multinational, Bolt Food da kuma kamfanin hada allura na ‘Jubilee Syringe Manufacturing’.
A ra’ayinmu, tsare-tsaren Babban Bankin Nijeriya CBN a ‘yan shekarun nan bai taimaka ba wajen zaburar da bunkasar kamfanoni da tattalin arzikin Nijeriya ba.
Masu harkokin fitar da kayyakin da ake sarrafawa a Nijeriya suna fuskanta rashin tabbas, basu da damar samun kudaden kasashen waje don gudanar da harkokin kasuwancinsu wanda haka ya taimaka wajen durkushewarsu.
Wani abin takaicin kuma shi ne tsaretsaren da aka samar don dakile hauhawar farashi ya taimaka ne kawai weajen takura kanana da mastaikaitun kamfanoni a fadin tarayyar kasar nan.
A irin wannan yanayin harkokin kasuwanci ba za su samu kwarin gwiwar ci gaba ba, kamar yadda kungiyar masu masana’antu ta zayyana a wani taron shugabannin kamfanoni da aka yi kwanakin baya ta yi.
Kungiyar ta yi hasashen wadannan kalubalen za su ta’azzara har zuwa zango na biyu na sabuwar shekara 2024, ana kuma iya samun farfadowa dan kadan daga baya. A hasashen nasu bangaren masana’antu zai samu bunkasar kasa da kashi 3.2 a wannan shdekarar, yayin da gudumawar bangaren ga tattalin arzikin kasa zai gaza kashi 10.
In har ana son kauce wa fadawa wadannan mastalolin dole a canza tsare-tsaren tattalin arzikin kasa ta yadda zai taimakawa bunkasar harkokin kasuwanci a Nijeriya. Muna bayar da shawara ga Babban Bankin Nijeriya ya bar matsayin harkokin kasuwanci ta nema wa naira daraja, a kuma dawo da ba masu masana’antu muhimmanci a wajen bayar da kudaden kasashen waje. Ya kuma kamata a rage ruwan da ake dorawa basukan da ake ba masu kanana da manyan masana’antu, hakan zai kara jawo masu zuba jari na ciki daga kasashen waje.
Samar da ingantaccen wutar lantarki, ta hanyar sake yi wa sashin garambawul zai matukar taimakawa zai kuma karfafa bunkasar masana’antunmu a cikin wannan shekarar.
Haka kuma ya kamata gwamnatin shugaba Tinubu ta ta tabbatar da an aiwatar da tanade tanaden da ke cikin kasafin kudin 2024 musamman bagarorin da suka nemi ba masu masana’antu tallafin kudade don samar da daidaito ga tattalin arzkin Nijeriya.
Muna kuma karfafa bukatar ‘yan Nijeriya su rika amfani da kayyakin da aka sarrafa a cikin gida, ya kuma kamata gwamnati ta jagoranci wannan yunkurin ta hanyar umartar hukumomi da ma’aikatun gwamnati su rika sayen kayayyakin da aka sarrafa a cikin gida, ta haka za a iya kauce wa durkushewar kamfanoni a wannan shekarar ta 2024.