Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa an samu tsananin fatara da yunwa da kuma rashin tsaro a Nijeriya a halin yanzu sakamakon gazawar gwamnati na kasa sauke nauyin da tsarin mulki ya dora mata na kare rayukan mutane da dukiyoyin al’ummar Nijeriya.
Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta sakamakon kashe-kashen ‘yan bindiga da aka samu a Abuja tsakanin ranakun Asabar da Lahadi.
- NIS Shiyyar Arewa Maso Gabas Ta Kaddamar Da “Operation Tsaron Iyaka”
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Satar Keke-napep A Kano
A cewar Atikun, muddin gwamnati ta gaza kare rayukan mutane da dukiyoyinsu, to lallai za a ci gaba da samun tsananin rashin tsaro a cikin kasar nan.
Ya ce, “Yadda ake ci gaba da samun tashin hankali a kasar nan yana mutukar damuna, musamman ma yadda ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane suke cin karensu babu babbaka.
“A kulluma ana kashe mana matasa da mutanen da ba su ji ba su gani ba. Ko a ranar Asabar ma sai da muka rasa Nabeeha wacce aka yi garkuwa da ita. Haka kuma a ranar Lahadi mun rasa mutane da dama ci har da dalibi mai suna Folorunsho Ariyo, dan shekara 13.
“Folorunsho yana daya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a rukunin gidaje na Sagwari da ke Dutse a karamar hukumar Bwari na Abuja a ranar 7 ga watan Janairun 2024.
“Tsananin talauci da yunwa yana kara karuwa ne a daidai lokacin da masu garkuwa da mutane ke haddasa rashin tsaro a Nijeriya, musamman ma a Abuja, Babbar Birnin Tarayya.
“A duk lokacin da gwamnati ta gaza sauke hakkin da tsarin mulki ya dora mata na tsare rayukan mutane da kuma dokiyoyinsu, za a samu ci gaba da ayyukan masu garkuwa da kuma sauran manyan laifuka a gidaje da otal-otel a garuruwa. Wannan babban abun takaici ne a kasar nan.”
Atiku ya kara da cewa wajibi ne ga hukumomi su dauki matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar tsaro cikin gaggawa domin sanya aminci a zukatan ‘yan Nijeriya.