Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada tabbacin yin aiki tare da Cibiyar Ƙwararru Kan Hulɗa Da Jama’a Da Yaɗa Labarai (NIPR) wajen tsare-tsaren hanyoyin sadarwar da za su tabbatar da cimma nasarar Ajandar Sabon Ƙudiri ta gwamnatin Tinubu.
Idris ya yi wannan tabbaci ne lokacin da ya ke jawabi a wurin rantsar da mambobin Hukumar Gudanarwar NIPR a ranar Talata a Abuja.
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Yaba Da Abota Da Goyon Bayan Juna Da Togo
- AFCON 2023: Tauraron Super Eagles Na Fama Da Guba Gabanin Wasa Da Cote d’Ivoire
Wannan bayani ya na ƙunshe a cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Minista, Rabi’u Ibrahim ya fitar a ranar Talata.
Idris ya ce: “A matsayi na na ɗan wannan cibiyar, na fahimci muhimmancin kare martaba da ƙima. To kuma Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai ta ƙudirta yin aiki tare da wannan cibiya domin shata tsare-tsaren sadarwa da yaɗa labarai, waɗanda za su zaburar da Ajandar Sabon Ƙudiri ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
“Tilas in bayyana maku cewa na yi matuƙar gamsuwa da irin tsare-tsaren da majalisar NIPR ta fito da su, a ƙarƙashin Dakta Ike Neliaku, kamar yadda aka nuna min kafin fara wannan taron.
“Ina da yaƙinin cewa matuƙar aka aiwatar da waɗannan tsare-tsare, to duk su na da karsashin da za su ɗabbaƙa wannan cibiya, kuma su ɗaukaka wannan ƙasa a idon duniya.”
Ministan ya ɗora wa cibiyar nauyin sake farfaɗo da ƙima da martabar Nijeriya a duniya, ya ce darajar kowace ƙasa ita ce tushe ko ginshiƙin gina ƙasar.
Ya ƙara da cewa daga cikin ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta, akwai abin da ya kira rashin ɗaukar ‘yan ƙasar da ita kan ta ƙasa da wata ƙima. Wannan kuma a cewar sa ba komai ya janyo hakan ba sai mummunar fassara da bahaguwar fahimtar da ake mana a faɗin duniya.
Ya ce: “Wannan kuma abu ne mai ɓacin rai a matsayin mu na ƙwararru. Don haka tilas mu bijiro da hanyoyin da za su kasance mafita, waɗanda za mu nuna wa duniya irin baiwa, daraja, ƙima da martabar da wannan ƙasaitacciyar ƙasa Nijeriya ke da ita.
“Sauran ƙasashe ma kowace na da nata matsalolin, amma inda bambancin yake shi ne ta yadda su ke tunkarar daƙile wani aibi.
“Wannan kuwa abu ne da ake iya cimma nasarar sa ta hanyar haɗa kai tsakanin gwamnati da ƙwararru irin NIPR da kuma kishin ‘yan ƙasa.”
Daga nan ya jinjina wa nagartattun mutanen da su ka kafa cibiyar shekaru 60 da su ka gabata, ta yadda yanzu har ta na ɗaya daga cikin cibiyoyin ƙwararru ƙalilan da ake da su a duniya, waɗanda gwamnati ta yi amanna da su ɗari bisa ɗari.