Darakta a Cibiyar Samar Da Ci Gaba Da Wanzar da Mulkin Dimokuradiyya (CDD), Idayat Hassan ta ankarar da cewa, haramtattun kudaden da ke yawo a nahiyar Afirka a yanzu sun karu zuwa Dala Biliyan 80.
Wannan bayanin na Idayat Hassan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar kare muradun nahiyar Afirka wato AU ke bikin zagayowar ranar yaki da cin hanci da rashawa.
- Zaben Gwamnan Osun: PDP Ta Zargi APC Da Shirin Amfani Da ‘Yan Bangar Siyasa
- Jaridar Daily Trust Ba Ta Yi Mana Adalci Ba- Fadar Shugaban Kasa
A cewarta, cin hanci da rashawa da kuma yadda haramtattun kudaden ke kara yawo a nahiyar Afirka na ci gaba da janyo wa nahiyar ci baya.
Idayat Hassan ta kara da cewa yana da kyau a sani cewa ta hanyar cin hanci da rashawa da kima yadda aka yi alumbazzaranci da kudaden tallafi na yakar annobar Korona a nahiyar Afirka, hakan ya kara samar da wata kafa wajen kara samun yawon haramtattun kudaden a nahiyar Ta Afirka.