• English
  • Business News
Tuesday, August 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Halin Da Wasu Jam’iyyun Siyasa Suka Tsinci Kansu

by Alhaji Adamu Rabiu
2 years ago
in Labarai
0
Halin Da Wasu Jam’iyyun Siyasa Suka Tsinci Kansu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

‘Yan Kasuwa Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

ASUU Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Rashin Cika Mata Alƙawura

Jam’iyyun siyasa 18 ne suka yi rijista da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), a lokacin da aka gudanar da babban zaben shekarar 2023. Koda-yake, guda bakwai ne kadai a cikinsu suka iya samun kujeru daga kan zaben shugaban kasa, gwamnoni, majalisun dokoki na kasa da kuma majalisar jiha. Wadannan jam’iyyu sun hada da APC, PDP, LP, NNPP, SDP, APGA da kuma YPP.

Gasa Da Kece Raini

‘Yan takara 18 ne suka nemi kujerar shugabancin kasa, inda har ila yau kimanin ‘yan takara 1,904 suka fito neman kujerun majalisar dattawa, wadda take da membobi 109. Kazalika, kimanin ‘yan takara 3,244 ne suka nemi kujerun majalisar wakilan kasar nan mai dauke da membobi 435, sannan ‘yan takara 416 ne suka nemi kujerun gwamnoni a jihohi 28 da aka gabatar da wadannan zabubbuka, yayin da kuma ‘yan takara kusan 10,240 suka fito neman kujerun majalisar jihohi 990a fadin jihohin Nijeriya.

Adadin kafatanin kujerun da aka fafata wajen zawarcinsu a zaben 2023, sun kai kimanin 2,533, yayin da kiyasin 16,808 suka fafata domin neman kujeru daban-daban, a wannan takaitaccen bayani, banda batun zaben fitar da gwani na gwamnoni da kuma na majalisun jihohi guda takwas.

Har ila yau, a kujerun shugabannin kananan hukumomi 774, a kowace jam’iyya akwai dan takara guda daya, wanda idan aka lissafa zai bayar da ‘yan takarkaru kimanin13,932, haka nan kididdigar kujeru 14,500 na kansiloli, wanda zai tasamma kimanin ‘yan takara 70,000 na wadannan jam’iyyun siyasa 18 da ake da su a fadin kananan hukumomi 774.

Kazalika, APC da PDP sun samu sama da kashi 90 cikin 100 na kujeru a matakin tarayya da jihohi, yayin da sauran suka samu kashi 10 cikin 100; inda kuma mafi yawansu suka kasa samun wata kujera ko yin wani gagarumin tasiri.

Halin Manyan Dawakai

– Kudade da albarkatu masu yawa: Manyan jam’iyyun, sun samu damar samun makudan kudade daga wurare daban-daban. Sannan, sun kuma samu damar kashe makudan kudaden a wajen yakin neman zabe tare da yin tasiri ga masu kada kuri’a. Abin taikaici a nan shi ne, wasu naira dari kacal suka karba, wasu kuma taliyar indomi domin zaben dan takara.

– Rashin tsari da iya warware rikici. Kamar yadda ta faru, ga wasu  babu tsari amma sun samu damar warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu tare da gabatar da dan takara guda daya tilo, ko dai ta tilastawa ko kuma wani nau’i na matsin lamba.

Matsalolin Kananan Dawakai

– Rashin isassun kudade da kayan aiki: Wasu ba su da isassun kayan aiki domin gudanar da yakin neman zabe, haka nan biyan kudaden tallace-tallacen kafafen yada labarai, shirya tarurruka tare da tara magoya bayansu. Har ila yau, ba su da isassun kayan aiki da kayayyakin more rayuwa, don isa ga masu kada kuri’a a fadin kasar baki-daya.

– Karancin  goyon bayan jama’a: Kananan jam’iyyun siyasa ba su da isasshen wakilci ko tasiri a cikin kafofin watsa labaru, kungiyoyin jama’a da sauran dandamali wadanda za su iya taimakawa wajen samun nasara a zabe.

– Rikicin cikin gida da rarrabuwar kai: Sau da dama suna fama da rikice-rikicen cikin gida da rarrabuwar kawuna, wanda ya raunana damar samun nasara. Wasu daga cikin jam’iyyun kuma sun fuskanci rikicin shugabanci da sauran makamantansu.

– Rashin adalci a zabuka: Ko shakka babu, kananan jam’iyyu sun fuskanci cikas da kalubale daban-daban a harkar zabe. Wasu daga cikin kalubalen sun hada da tashe-tashen hankula da kuma tsoratarwa, wanda ya hada da magudi, satar kuri’u, sayen kuri’u da kuma rashin ingancin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), da kuma dokar zabe da sauran makamantansu.

Tasiri a nan gaba

  • Shin kananan jam’iyyu za su iya yin tasiri a irin wannan yanayi na siyasa da a ciki?
  • Shin akwai hikima a fannin tattalin arziki a ci gaba da wannan harkar ko kuwa manyan dawakai ne ke ciyar da kananan dawakai?
  • Shin dabi’ a ce mai kyau a cikin dabi’u a koyaushe a ga ‘yan siyasa suna tsalle daga wannan jamíya zuwa wancan kamar yadda ya ke faruwa a Nijeriya yanzu, sannan ya kamata ‘yan Nijeriya su amince da hakan?

Inna mafita

Shin zai yiwu a kubutar da ’yan Nijeriya yayin da ake ganin kamar sun samu kwanciyar hankali a cikin bautar da suke ciki?

–      Eh, mai yiyuwa ne a fita daga wannan mawuyacin hali da rugujewar akidar siyasa, inda kashi 90 cikin 100 na ‘yan siyasar Nijeriya, ba kasar ce a gabansu ko ‘yan kasar ba, sai san kansu da zalunci.

–      Bugu da kari, ya rage wa sauran kashi 10 cikin 100 na ‘yan siyasa masu hankali da kishin kasa da su canza salon siyasar kasar, domin talaka ya samu ya numfasa.

  Bayanan karshe

Tarihi ya nuna sau da dama an fi samun ‘yan siyasar da ke rike da madafun iko, bayan sun sauka ko kuma damar ta kubuce musu su zama abun tausayi, ko samun kansu cikin wani yanayi na lahaula ko wani abu mai kama da haka.

Kukan kurciya dai hausawa sun ce jawabi ne.

Alhaji Adamu Rabiu, ya rubuto daga Kaduna.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Ina So A Rika Tunawa Da Ni A Kan Kyawawan Halaye Da Cika Alkawari – Fatima Abdullahi

Next Post

AFCON 2023:Tanzania Ta Kori Kocinta Bayan Rashin Nasara A Hannun Maroko

Related

‘Yan Kasuwa Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas
Manyan Labarai

‘Yan Kasuwa Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

1 hour ago
Yajin Aikin ASUU Na Barazana Ga Ci Gaban Kasa
Labarai

ASUU Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Rashin Cika Mata Alƙawura

3 hours ago
Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka
Ra'ayi Riga

Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

4 hours ago
Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya
Rahotonni

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

6 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Gargadin Jihohin Arewa 9 Kan Afkuwar Ambaliya 

15 hours ago
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3 Da Kubutar Da Mutum 16 Da Aka Sace A Kaduna
Labarai

ECOWAS Za Ta Kaddamar Da Rundunar Yaki Da Ta’addanci Mai Jami’ai 260,000

16 hours ago
Next Post
AFCON 2023:Tanzania Ta Kori Kocinta Bayan Rashin Nasara A Hannun Maroko

AFCON 2023:Tanzania Ta Kori Kocinta Bayan Rashin Nasara A Hannun Maroko

LABARAI MASU NASABA

Saka Zai Yi Jinyar Makonni 4 Sakamakon Rauni Da Ya Samu A Wasan Leeds

Saka Zai Yi Jinyar Makonni 4 Sakamakon Rauni Da Ya Samu A Wasan Leeds

August 26, 2025
‘Yan Kasuwa Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

‘Yan Kasuwa Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

August 26, 2025
ÆŠaruruwan ‘Yan APC Sun Koma ADC A Sakkwato Saboda Rashin Tsaro Da Talauci

ÆŠaruruwan ‘Yan APC Sun Koma ADC A Sakkwato Saboda Rashin Tsaro Da Talauci

August 26, 2025
Yajin Aikin ASUU Na Barazana Ga Ci Gaban Kasa

ASUU Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Rashin Cika Mata Alƙawura

August 26, 2025
Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

August 26, 2025
ÆŠan Nijeriya Ya Lashe Lambar Azurfa A Gasar Ninkaya Ta Duniya

ÆŠan Nijeriya Ya Lashe Lambar Azurfa A Gasar Ninkaya Ta Duniya

August 26, 2025
Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

August 26, 2025
An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

August 25, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

August 25, 2025
CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

August 25, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.