Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara, ya ce haddar Alkur’ani mai girma da karatun Alkur’ani za su taimaka matuka gaya wajen bunkasar kwakwalwa ga masu karatu musamman matasa.
Ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su tabbatar da karantawa da haddar hadisan Annabi (S.A.W.).
- Ya Sace Katan 20 Na Alkur’ani Da Hadisai A Kwara
- An Bizne Gawar Jakadan Nijeriya Na Kasar Faransa A Jihar Kwara
Gwamnan ya yi wannan jawabi a ranar Lahadin da ta gabata a garin Ilorin a wajen rufe gasar karatun Alkur’ani da Hadisi da ofishin kula da al’adu na ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja da kuma Cibiyar Da’awah da Bincike ta As-Sunnah da ke Ilorin suka shirya a Jihar Kwara.
Gwamnan ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Farfesa Mamman Saba Jibril.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa gasar ta kunshi bangare shida, kowanne bangare ya kunshi hazikan dalibai da mahaddata Alkur’ani da Hadisi.
Manyan daliban da aka gwabza da su a wannan rana sun hada da Abdulrahman Ismail da Ahmad Abdulsalam da Abdullateef Zakariyya da Khadijah Ajijolakewu da Zainab AbdulGafar da Naeem Abdulsalam da Usman Ayinde da Kamaldeen Suleiman da Abdulmajeed Abdullateef.
Sauran sun hada da Ahmad Abdulazeez da Muslimah Abdullateef da Sofiyullahi Murtadha da Maryam Abdulkareem da Maiyaki Muktar; Salimah Abubakar da Aisha Abdulrahman da Zainab Abubakar da kuma Ali Muhammad.
Gwamnan ya ce, ya zama wajibi ga Musulmi musamman matasa su ci gaba da neman ilimin Alkur’ani da Hadisi, tare da haddace su don ciyar da addinin Musulunci gaba da kuma jagorantar rayuwarsu.
AbdulRazaq ya bayyana littafin a matsayin tushe na dukkan ilimi, ya kuma dora wa masu imani da su sadaukar da kansu wajen karatu da nazarinsa akai-akai, yayin da yake taya wadanda suka shirya gasar da kuma wadanda suka yi nasara daban-daban murnar samun nasarar gudanar da gasar.
Ya kuma yi alkawarin gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da yanayi da zai ba da damar zaman lafiya da a tsakanin mabiya addinai a jihar.