Rundunar ‘yansanda a Jihar Kwara ta cafke wani mutum mai suna Mustapha Jimoh da ke unguwar Amoyo ta Karamar Hukumar Ifelodun bisa zargin satar katan 20 na littattafan addinin Musulunci da suka kunshi Al-Kur’ani da Hadisan Manzon Allah. Sallallahu Alaihi Wasallam.
Majiyarmu ta nakalto cewa wanda ake zargin ya kutsa kai cikin dakin karatu na wani malami dan kasar Saudiyya, Ustaz Jamiu, don sato kayan.
- Gazawar Gwamnati Ta Tsananta Fatara Da Rashin Tsaro A Nijeriya –Atiku
- Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Nasir Idris A Matsayin Gwamnan Jihar Kebbi
Wata majiya ta ce, “Lokacin da Ustaz Jamiu mazaunin Ganmo ya dawo gida ya ziyarci iyalinsa, sai ya gano dakin karatunsa dake daura da gidansa an bude shi. Kimanin Katan 20 na Alkur’ani da Hadisi da suka hada da wasu kayayyaki da aka kiyasta kudin sun kai Naira miliyan 2.7, aka gano an sace su.”
Da take tofa albarkacin bakinta, kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar wa wakilinmu afkuwar lamarin, inda ta ce, “Wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne bayan kama shi, yayin da kuma aka kama sauran wadanda ake zargi.”