A yayin da ake gudanar da taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na shekara-shekara na shekarar 2024 a garin Davos na kasar Switzerland, wakiliyar CMG ta yi hira da Klaus Schwab, wanda ya kafa dandalin kuma shugabansa, inda ta yi masa tambayar cewa, “Me ya sa aka zabi “sake gina aminci” a matsayin jigon taron?”
Schwab ya bayyana cewa, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, duniyarmu ta rarrabu, an rasa aminci ga juna. Ban da haka, a karkashin matsin lamba daban-daban, a mai da hankali a kansa kawai. Shi ya sa ana fatan gina sabon ruhi yayin da hakan ya kasance makasudin taron na shekara-shekara. A sa’i daya kuma, hagen nesa da kuma ba da fifiko ga aminci, shi ma dalili ne da ya sa aka zabi “sake gina aminci” a matsayin jigon taron.
Shi ya sa, jigon nan yana da wata manufa daya da bangarori biyu. Na farko shi ne sake gina aminci nan gaban. Na biyu shi ne kowa ya tunatar da kansa cewa, mu “na dogara” ne da al’ummomin duniya da na makomar duniya, da kuma “masu dogaro” da muhallin halittu. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp