Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin raya birnin Fuzhou na tsawon shekaru 20 mai lamba 3820 a shekarar 1992 yayin da yake mukamin sakataren kwamitin JKS na birnin. Inda ya mai da muradun jamaa a gaban komai yayin da ya tsayar da manufofin raya birni da kiyaye muhalli da aikin ba da ilmi da aladu da sauransu.
A cikin shekaru 30 da suka gabata, birnin na ci gaba da yin riko da tunaninsa, don daga matsayin zaman rayuwar jamaa.
- Xi Ya Amsa Wasikar Da Daliban Kenya Da Suka Yi Karatu A Jami’ar Beijing Jiaotong Suka Rubuta Masa
- Shugaban Kasar Sin Ya Ba Da Umarnin Ceton Mutanen Da Suka Bace A Zaftarewar Kasa Ta Kudu Maso Yammacin kasarÂ
Gidajen kwana muhimman moriya ne ga jamaa, suna da alaka da zaman rayuwa har ma raya birnin, wanda an dade ana mai da hankali kan wannan batu bisa tsarin 3820. Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya bayyana cewa, dole ne a raya tattlin arziki tare da kiyaye muhalli, ba za a iya raba su ba.
A shekarar 1995, Xi Jinping ya shaidawa manema labarai cewa, aikin da ya fi gamsar da shi, shi ne aikin gamsar da jamaa. Ya ce, yana gamsar da ayyukan da aka tabbatar dake da alaka da zaman rayuwa da zamantakewar jamaa. (Amina Xu)