Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana goyon bayansa ga matakin da babban bankin ya dauka na mayar da wasu ma’aikatunsa biyar daga babban birnin tarayya Abuja zuwa jihar Legas.
Sanusi ya soki masu adawa da matakin, inda ya bayyana matsayinsu a matsayin wata illa ga makomar bankin.
- CBN Ya Ruguza Shugabannin Gudanarwar Bankunan Union, Keystone, Polaris Da Titan Trust
- Mayar Da CBN Legas: Muna Roko A Mayar Da Ma’aikatar Kasuwanci Kano, NNPCL, NIMASA, NPA Zuwa Neja Delta
Ya kuma jaddada mahimmancin fifita bukatun bankin fiye da bukatun kai da ake so na ci gaba da zaman ma’aikatun a Abuja.
Sanusi ya yi nuni da cewa, da yawa daga cikin ma’aikatan CBN ’ya’yan ’yan siyasa ne wadanda ke fifita salo da jin dadin rayuwarsu da kasuwanci a Abuja fiye da nauyin da ke kansu na aikin bankin.
Ya yi imanin cewa, mayar da wasu sassan bankin zuwa babban ofishinsa da ke Legas zai inganta aikin da kuma rage adadin kudin gudanar da bankin.
A cikin shawarwarin nasa, Sanusi ya ba da shawarar mayar da sashen kula da harkokin kudi (FSS) da kuma galibin sashen ayyuka zuwa Legas, inda mataimakan gwamnan biyu za su gudanar da aikinsu daga can.
Ya kara ba da shawarar cewa, sassan da ke ba da rahoto kai tsaye ga Gwamnan bankin da ofishin Gwamnan Bankin da su ci gaba da kasancewa a Abuja.