Kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar adawa ta PDP wanda uwar jam’iyyar ta turo Jihar Katsina domin daidaita al’amurra, ya ce zai mayae da hankali kan abubuwa guda uku daga cikin har da haɗa kan ‘yan jam’iyyar domin shafe tasirin sauran jam’iyyu.
Shugaban kwamitin rikon kwaryar, Alhaji Musa A. Karim, ya bayyana haka jim kadan bayan sun kammala taro da mambobin jam’iyyar.
- Tinubu Zai Kori Ministocin Da Ba Su Da Kwazon Aiki – Hadiza Bala Usman
- Sanusi Ya Amince Da Mayar Da Wasu Ma’aikatun CBN Zuwa Legas
Ya ce bayan tattara hankalin ‘ya’yan jam’iyyar waje guda, za su tabbatar sun sasanta duk wani sabani da sauran bangarori da suka samu rashin fahimtar juna a baya.
“Muna da kalubale a wannan jam’iyya ta PDP a Katsina, amma hakan ba zai hana mu ba samun kwarin gwiwa wajen ganin mun dawo da martabarta a Jihar Katsina ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa abu na uku da jam’iyya ke fuskanta shi ne zaben cike gurbi da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta gudanar a watan Fabrairu, 2024, wanda ya shafi dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Sabuwa da Kankara da kuma Faskari.
Idan za a yi tunawa dan takarar majalisar tarayya karkashin jam’iyar APC a zaben 2023, Honarabul Dalhatu Shehu Tafoki ya kai karar Hon. Jamilu Mohammed Lion, wanda INEC ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.
Karim, ya ci gaba da cewa wannan kwamiti na rikon kwarya zai tabbatar da nasarar jam’iyyar PDP a zaben da za a sake.
Kwamitin na mutum 15 da suka hada da Hon. Musa A. Karim shugaban jam’iyyar PDP da Hon Sanusi Ali da Hon. Abubakar Lawal da Hon. Abubakar Yusuf da Hon. Ibrahim Assalamu Alaikum da Hon. Nura Gambo da Hon. Tijjani Mashasha.
Sauran sun hada da Hon. Ubaida Jafar da Hon. Lawal Magaji Ɗanɓaci da Hon. Danjuma Altine da Hon. Haruna Garba, (Dogo na Maraya) da Hon. Ibrahim Tafashiya da Hon. Ubaida Mai’adua da Hon. Shitu Magami da kuma Halina Zubairu Ɗanbata a matsayin sakatariyar rikon kwarya ta jam’iyyar PDP a Katsina
Jam’iyyar PDP dai a Jihar Katsina na fama da rikicin da ya kai ta ga rashin nasarar zaɓe5n gwamnan da ya gabata tare rasa wasu kujerun ‘yan majalisar tarayya a jihar.