Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum Alhamis din nan cewa, kasar Sin ta kadu da harin da aka kai kan cibiyar MDD a zirin Gaza, kuma ta yi matukar bakin ciki da hasarar rayukan fararen hula da harin ya haddasa. Sin na kira ga dukkan bangarorin da ke rikici, da su hanzarta dakatar da tashin hankali don hana tsanantar bala’in jin kai.
Bayanai na cewa, harsashen tankokin yaki sun fada kan wata cibiyar MDD dake samar da horo ga ‘yan gudun hijirar Falasdinu a yankin Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 9 tare da jikkata 75.(Ibrahim)