Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta ce ta kama mutum 16 da ake zargi da aikata miyagun laifuka da kuma garkuwa da mutane a Abuja, Babban Birnin Kasar.
BBC ta rawaito cewa, hakan ya biyo bayan kaddamar da rundunar ‘yansanda ta musamman da Sufeto-Janar na ‘yansanda, IGP Kayode Egbetokun, ya yi kwanan nan, inda har suka samu nasarar kama mutanen gami da kwato makamai da alburusai a Babban Birnin Tarayya Abuja.
- Kasashen Afirka 10 Da Za Su Samu Bunkasar Tattalin Arziki A 2024
- ‘Yansandan Sun Ceto Mutane 14, Sun Kashe Dan Bindiga A Nasarawa
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan ta Nijeriya, Muyiwa Adejobi ya fitar, ya ce rundunar hadin gwiwa ta jami’ansu sun kuma kama wasu mutum 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
Daga cikin wadanda aka kama a ranar Asabar din, akwai wasu masu garkuwa da mutane uku, wadanda kuma ake zargi da aikata fashi da makami a karamar hukumar Bwari da sauran sassan Abuja.
“Daga cikin nasarorin da aka samu akwai yadda aka dakile wani shirin yin garkuwa da mutane ta hanyar leken asiri wanda ya yi sanadin kama masu garkuwa da mutane a Bwari, da kwato makamai daga hannunsu,” in ji sanarwar.
Haka-zalika, ‘yansandan sun cafke wani mai sayar da bindigogi mai suna Eberest Magaji, a lokacin da yake tattaunawa da wasu gungun ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a yanzu, domin sayar musu da muggan makamai da alburusai.
Sun ce sun kwato bindiga kirar pistol guda 11, da kuma harbi-ruga biyu daga hannun wanda ake zargin.