Alkaluman da hukumar bayar da kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar a yau Asabar, sun nuna cewa, jimilar ribar manyan masana’antun samar da kayayyaki da hidimomi na kasar, ta karu cikin watanni 5 a jere zuwa watan Disamban shekarar 2023.
Hukumar ta ce, ribar manyan masana’antun dake samun kudin shigar da ya kai akalla kudin Sin RMB yuan miliyan 20 a shekara, kwatankwacin kimanin dalar Amurka miliyan 2.8, ta karu da kaso 16.8 a watan Disamban bara.
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Zai Tattauna Da Mashawarcin Shugaban Amurka Kan Tsaro Yayin Ziyararsa A Thailand
- Shugaban Kasar Tunisiya Ya Gana Da Wang Yi
A shekarar 2023, ribar manyan masana’antun ta kai yuan triliyan 7.69, wadda ta ragu da kaso 2.3 kan na shekara-shekara, inda matakin raguwar ya ragu da maki kaso 2.1 daga watanni 11 na farko.
A cewar NBS, bangaren samar da lantarki da na’urorin dumama wuri da gas da samar da ruwa da kayayyaki, su ne suka fi samun tagomashi a bara, inda suka samu ribar da ta karu da kaso 54.7. Tagomashin da suka samu ya karawa ribar da baki dayan bangaren masana’antar samar da kayayyaki da hidimomi ya samu da maki kaso 3.1.
Bugu da kari, ribar da bangaren samar da kayayyakin aiki ya samu, ta karu da kaso 4.1 a bara, maki kaso 2.4 sama da wadda aka samu shekara guda kafin sannan. (Fa’iza Mustapha)