Biyo bayan daukaka karar da ‘yar takarar jam’iyyar APC a zaben 2023 a Jihar Adamawa, Aishatu Dahiru Binani, ta yi kotun Koli ta sanar da ranar 29 ga watan Janairu 2024, a matsayin ranar da za ta saurari shari’ar.
Binani ta shigar da kara a gaban kotun kolin, inda kalubalanci hukuncin kotun daukaka kara da hukumar zabe INEC da ta ayyana gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamna a Jihar Adamawa.
- Ganduje Ya Zargi ‘Yan Siyasa Da Hannu A Haddasa Rikice-rikicen Zabe
- INEC Ta Bukaci A Samar Da Tsaro A Yankunan Zaben Cike Gurbi
Majiyoyi sun bayyana cewa kotun ta aike da sanarwar sauraron karar ga lauyoyin bangarorin da shari’a ta shafa, cewa za ta saurari shari’ar ranar Litinin mai zuwa.
Jihar Adamawa, ita ce jiha daya tilo daga cikin jihohin Nijeriya da Kotun Koli ba ta kai ga yanke hukunci kan shari’ar kujerar zaben gwamnan ba.
A baya dai kotun kolin ta yanke hukunci kan zaben gwamnonin jihohin Kano, Zamfara, Bauchi, Filato, Nasarawa, Ribas, Legas, Delta da dai sauransu.