Shugabannin kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso sun sanar da ficewa daga kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS) cikin gaggawa domin nuna adawa da matakin dakatar da su daga kungiyar.
Shugabannin kasashen uku na yammacin Afirka sun fitar da wannan sanarwar ne a ranar Lahadi, inda suka ce ” wannan hukuncinsu ne” na barin kungiyar ECOWAS cikin gaggawa “ba tare da bata lokaci ba”.
- Jami’an Tsaro Sun Kama Ɗan Bindigar Da Ake Zargi Da Kashe Nabeeha
- Zan Bar Barcelona A Karshen Kakar Wasanni Ta Bana-Xavi
Kasashen na alaka da ECOWAS ne saboda fama da tashe-tashen hankula da fatara da fama da masu da’awar jihadi a yankunan, amma tun bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar a ranar 26 ga Yuli, 2023, Burkina Faso a 2022 da Mali a shekarar 2020, ECOWAS ta dakatar da kasashen daga cikin jerin mambobinta.
Kungiyar ECOWAS ta dakatar da kasashen uku daga kungiyar, inda Nijar da Mali ke fuskantar tsauraran takunkumi.