Gwamnatin jihar Jigawa ta kammala shirye-shiryen mayar da dalibanta 194 da yakin basasa a Sudan ya tarwatsa su zuwa kasar Cyprus da Indiya domin ci gaba da karatun likitanci.
Da yake jawabi ga daliban da iyayensu a gidan gwamnatin da ke babban birnin jihar, Dutse, gwamnan jihar Malam Umar Namadi ya ce, tun bayan barkewar yakin basasa a kasar Sudan, gwamnatin jihar Jigawa ta na ta bibiyar irin halin da kasar ke ciki.
- Kotun Ƙoli Ta Jingine Hukuncin Zaɓen Gwamnan Adamawa
- Harin Tudun Biri: Nan Da Makonni Biyu Za A Fara Sake Gina Sabon Garin Tudun Biri – Gwamna Sani
Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Jigawa tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya sun yi namijin kokari wajen ganin an kwashe dalibanta da jihar ta dauki nauyin karatunsu lafiya, kuma an yi nasarar dawo da su Nijeriya lafiya.
“Sai dai tun bayan dawowar daliban gida, gwamnati ta ci gaba da aiki ba dare ba rana don ganin an sake samun gurbin karatu ga daliban a jami’a mai inganci don ci gaba da karatunsu kuma domin cimma burinmu na samun isassun ma’aikata da za su kula da harkokin kiwon lafiya a jiharmu.
“A yau ma’aikatar ilimi ta jiharmu, ta samu nasarar samar wa dalibai 184 guraben karatu a jami’ar Cyprus da kuma 10 a jami’ar Indiya, kuma an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace na jigilarsu zuwa kasashen a ranar 5 ga watan Fabrairu,” in ji Gwamna Namadi.