Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da karbar wasu muhimman kayyayaki gabanin zaben cike gurbi da za a sake gudanarwa a ranar Asabar a jihar Kaduna.
Malam Aminu Idris, Kwamishinan Zabe na INEC a jihar, ya jagoranci tawagar masu ruwa da tsaki wajen baje kolin kayayyakin a ranar Litinin a harabar ofishin INEC da ke Kaduna.
- ‘Yansanda Ne Ke Bayar Da Babbar Gudunmuwar Satar Mutane A Nijeriya – Seun Kuti
- Gwamna Nasir Ya Amince Da Fitar Da Naira Miliyan 27.5 Don Biyan Kuɗin Ɗaliban Lauyoyi Na Jihar Kebbi
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, an shirya gudanar da zabe a mazabu 6 da suka kunshi kananan hukumomi bakwai da suka hada da Chikun, Igabi, Kaduna ta Kudu, Kudan, Kachia, Kagarko, da Kauru.
Jimillar rumfunan zabe a wadannan mazabu shida sun kai 1,114, kuma ana sa ran masu kada kuri’a 639,914 ne suka karbi katin zabe na dindindin (PVCs) a mazabun.
Wakilan INEC da masu ruwa da tsaki daban-daban ne suka halarci wurin baje kolin kayayyakin, wadanda suka hada da wakilan jam’iyya, jami’an tsaro, kungiyoyi masu zaman kansu (CSOs), da ‘yan jarida.