ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Ɗaure Tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan shekaru 10 A Gidan Yari

by Sulaiman
3 years ago
Pakistan

Kasa da mako biyu gabanin zaben Pakistan da ke tafe, a ranar Talata aka yankewa tsohon Firaminista Imran Khan hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari. Jam’iyyar Khan ‘Tehreek-e-Insaf (PTI)’ na fuskantar kalubale sosai a zaben da ke karatowa.

An yanke hukuncin ne a cikin gidan yarin Adiala, inda ake tsare da Khan tun lokacin da aka kama shi a watan Agustan 2023. Khan na fuskantar shari’o’in kotu da dama, wadanda ya ce, an kirkirar masa su ne domin hana shi tsayawa takara.

  • ‘Yansanda Ne Ke Bayar Da Babbar Gudunmuwar Satar Mutane A Nijeriya – Seun Kuti
  • Ma’aikatan CBN 1,500 Sun Koma Aiki A Ofishin Legas

Shah Mehmood Qureshi, mataimakin shugaban jam’iyyar PTI, kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar a karkashin Khan, shi ma an yanke masa irin hukuncin da aka yanke wa mai gidansa (Imran Khan).

ADVERTISEMENT

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, kakakin jam’iyyar PTI ya tabbatar da hukuncin, sannan kuma kafafen yada labaran kasar su ma sun ruwaito hukuncin.

Hukuncin dai da aka yanke musu na da alaka da zargin fallasa wasu bayanan sirri na kasar.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Dauda Ya Amince Da Ɗaukar Ƙarin Ƙwararrun Ma’aikata 75 A Hukumar Haraji Ta Zamfara

Zargin Yi Wa Tinubu Kamfen A Masallaci: Hukumar Shari’a Ta Bauchi Ta Gayyaci Limamin Da Aka Cire

Khan ya jagoranci al’ummar kasar tun daga shekarar 2018 har zuwa hambarar da shi a shekarar 2022 ta hanyar kada kuri’ar rashin amincewa, sakamakon rashin goyon bayan da sojoji suka yi masa.

Khan dai ya kasance mai sukar jami’an soji, inda ya zarge su da yunkurin kashe shi.

Dan rajin kare hakkin dan Adam kuma manazarcin siyasa Tauseef Ahmed Khan ya bayyana hukuncin a matsayin “rashin adalci,” yana mai cewa, wannan ba zai dusashe hasken Khan ba sai dai ma ya kara masa farin jini da soyayya.

Pakistan
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Ya Amince Da Ɗaukar Ƙarin Ƙwararrun Ma’aikata 75 A Hukumar Haraji Ta Zamfara
  • Sulaiman
    Soja Ya Samu Kyautar N500,000 Bayan Ya Ƙi Karɓar Cin Hanci
  • Sulaiman
    2027: Zan Magance Matsalar Tsaro, Na Farfaɗo Da Fatan ’Yan Nijeriya — Atiku
  • Sulaiman
    An Kai Wa Ayarin Motocin Peter Obi Da Kwankwaso Hari A Jihar Calabar

MASU ALAKA

Gwamna Dauda Ya Amince Da Ɗaukar Ƙarin Ƙwararrun Ma’aikata 75 A Hukumar Haraji Ta Zamfara
Labarai

Gwamna Dauda Ya Amince Da Ɗaukar Ƙarin Ƙwararrun Ma’aikata 75 A Hukumar Haraji Ta Zamfara

November 5, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Labarai

Zargin Yi Wa Tinubu Kamfen A Masallaci: Hukumar Shari’a Ta Bauchi Ta Gayyaci Limamin Da Aka Cire

November 4, 2026
Uwargidan Tinubu Na Tallafa Wa Mata Saboda Tausayi – Minista
Labarai

Uwargidan Tinubu Na Tallafa Wa Mata Saboda Tausayi – Minista

November 4, 2026
Next Post
Xi Ya Tayawa Azali Assoumani Murnar Sake Zaben Shugaban Comoros Ta Wayar Tarho

Xi Ya Tayawa Azali Assoumani Murnar Sake Zaben Shugaban Comoros Ta Wayar Tarho

LABARAI MASU NASABA

Taron Tattaunawar Magajin Gari Na Duniya Na 2026 A Ningbo Ya Kasance Na Bude Kofa Da Haduwa Da Juna Da Hadin Gwiwar Birane

Taron Tattaunawar Magajin Gari Na Duniya Na 2026 A Ningbo Ya Kasance Na Bude Kofa Da Haduwa Da Juna Da Hadin Gwiwar Birane

November 4, 2026
Gwamna Dauda Ya Amince Da Ɗaukar Ƙarin Ƙwararrun Ma’aikata 75 A Hukumar Haraji Ta Zamfara

Gwamna Dauda Ya Amince Da Ɗaukar Ƙarin Ƙwararrun Ma’aikata 75 A Hukumar Haraji Ta Zamfara

November 5, 2026
Li Qiang Ya Gana Da Darakta Janar Na Hukumar WIPO

Li Qiang Ya Gana Da Darakta Janar Na Hukumar WIPO

November 4, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Zargin Yi Wa Tinubu Kamfen A Masallaci: Hukumar Shari’a Ta Bauchi Ta Gayyaci Limamin Da Aka Cire

November 4, 2026
Uwargidan Tinubu Na Tallafa Wa Mata Saboda Tausayi – Minista

Uwargidan Tinubu Na Tallafa Wa Mata Saboda Tausayi – Minista

November 4, 2026
Han Zheng Zai Tafi Turkiye Don Halartar Taron Kolin Kasashen Da Suka Daddale Yarjejeniyar Sauyin Yanayi Ta MDD

Han Zheng Zai Tafi Turkiye Don Halartar Taron Kolin Kasashen Da Suka Daddale Yarjejeniyar Sauyin Yanayi Ta MDD

November 4, 2026
Yamal Ya Kwace Tarihin Mbappe A Gasar Zakarun Turai

Yamal Ya Kwace Tarihin Mbappe A Gasar Zakarun Turai

November 4, 2026
Soja Ya Samu Kyautar N500,000 Bayan Ya Ƙi Karɓar Cin Hanci

Soja Ya Samu Kyautar N500,000 Bayan Ya Ƙi Karɓar Cin Hanci

November 4, 2026
Yadda Manufar Soke Haraji Da Bikin CIIE Suka Fadada Hadin Gwiwar Cin Moriyar Juna Tsakanin Sin da Afirka

Yadda Manufar Soke Haraji Da Bikin CIIE Suka Fadada Hadin Gwiwar Cin Moriyar Juna Tsakanin Sin da Afirka

November 4, 2026
Tsadar Rayuwa: Yadda Iyalan Nijeriya Ke Komawa Abinci Mai Rahusa Domin Samun Sauƙin Rayuwa

Matsin Tsadar Rayuwa A Nijeriya: Abubuwa 10 Da Suka Ƙara Tsada A Zamanin Tinubu

November 4, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.