Kotun Koli ta kori karar da ‘yar takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar APC a babban zaben 2023, Sanata Aishatu Dahiru Binani, da ta shigar tana mai kalubalantar ayyana gwamna Amadu Umaru Fintiri, a matsayin gwamnan jihar Adamawa.
Kotun karkashin jagorancin Mai shari’a John Okoro, ta tabbatar da cewa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri shine halastaccen gwamna a jihar Adamawa.
- AFCON 2023: Yadda Afirka Ta Kudu Ta Hana Morocco Rawar Gaban Hantsi
- An Nada Mambobin Hukumar Jindadin Alhazai Mutum 10 A Adamawa
Haka kuma Mai shari’a John Okoro ya bayyana cewa matakin da Kwamishinan hukumar Zabe ta jihar (REC), Hudu Ari, ya dauka, wani aiki ne na rashin gaskiya da kuma aikata laifi.
Mai shari’a Okoro ya ci gaba da cewa, jami’i Mai sanar da sakamakon zabe ya kamata ya bayyana sakamakon zabe, domin a kaucewa hargitsi da rudani.
Ya bayyana cewa dokar zabe ta ba da alhakin wanda zai bayyana sakamakon zabe, kuma wannan iko ya rataya ne kawai ga jami’in da hukumar zabe INEC ta aiko Mai sanar da sakamakon zabe