Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce kasar ta kasance babbar abokiyar cinikayya ta nahiyar Afrika cikin shekaru 15 jere, inda darajar cinikayya a tsakaninsu ta kai dala biliyan 282.1 a shekarar 2023.
Wani jami’in ma’aikatar Jiang Wei, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, hadin gwiwa a bangaren tattalin arziki da cinikayya, shi ne ke ingizawa tare da habaka dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika.
- CMG Ta Yi Bayani Kan Shirye-Shirye Da Kirkire-Kirkiren Fasaha A Liyafar Bikin Bazara Ta 2024
- Kamata Ya Yi Amurka Ta Yi Dogaro Da Kanta Don Warware Matsalar Miyagun Kwayoyi
Majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince da shirin gina wani yankin gwaji domin zurfafa hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki tsakanin Sin da Afrika. Bisa tanadin shirin, kasar Sin za ta kafa yankin gwajin a matsayin dandalin bude kofarta da hadin gwiwa da nahiyar Afrika, ta yadda zuwa shekarar 2027, zai kai wani matsayin da zai yi tasiri a duniya.
A shekaru masu zuwa, bangarorin biyu za su taka rawar da ta dace wajen jagorantar yankin na gwaji da inganta samar da sauye-sauye da daukaka dangantakar tattalin arziki da cinikayya da samar da moriya ga al’ummun Sin da Afrika. (Fa’iza Mustapha)