Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta bayyana goyon bayanta na samar da ‘yan sandan jihohi, inda ta ce hakan zai magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan.
Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar, Bala Mohammed, ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a lokacin da ya jagoranci takwarorinsa a taron da suka kai wa Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato ziyara a gidan gwamnati da ke Jos.
Mohammed, wanda ya yi tir da yadda kalubalen tsaro ke kara tabarbarewa a fadin kasar, ya ce ‘yan sandan jihohi za su taimaka wajen kara kaimi ga kokarin da hukumomin tsaro ke yi.
A cewarsa, ‘yan sandan jihar za su bayar da dama ga gwamnonin su tafiyar da harkokin tsaro a jihohinsu cikin sauki.