‘Yan’uwa Musulmi Assalama alaikum warahmtullahi ta’ala wabarkatuh. Kafin mu shiga bayani game da yadda Allah Madaukakin Sarki ya rantse da darajar wanda ya fi so kaf cikin halittu baki daya, za mu karasa bayanin da muka faro a makon jiya kan yadda Allah (SWT) yake lallashin Manzon Allah (SAW) game da karyatawar da kafirai suka yi masa. Da kuma raddin da Allah ya yi musu. Sannan da takaitaccen bayani kan girman darajar Ma’aiki a wurin Allah ta fuskacin yadda yake masa alkunya tare da sakaya sunansa wurin kira sabanin irin yadda (Allah) yake wa sauran Annabawansa masu girma. Daga nan sai mu dora da darasinmu na wannan makon.
Allah ya kiyaye Manzon Allah (SAW) a yi masa lamba ta aibatawa. Allah ya zargi masu karyatawan da tsaurin kai tare da yin jayayya da ayoyinsa. Idan ka ji Larabawa sun ce mutum mai musu; suna nufin wannan mutumin ya fandare kana ya musa wani abu, ba musun ne kawai shi kadai tattare da sunan ba. A cikin ayar, Allah ya ba Manzon Allah (SAW) hakuri kana ya debe masa kewa ta hanyar rarrashinsa da cewa “ba shi ne kafiran suke karyatawa ba”. Allah ya kuma yi wa Manzon Allah (SAW) alkawari da nasara a ayar da ya ce “Hakika an karyata Manzannin da suka zo kafin kai sai suka yi hakuri a bisa abin da aka karyata su a kai kuma aka cuce su har dai taimakonmu ya zo musu, ba a canja kalmar Allah (cewa duk wanda aka aiko sai an karyata shi), to labarin Manzanni ya zo maka (naka ma ya fi sauki)”.
Malam Farra’u (Malamin Nahwu) da Malam Kisa’i (Malami Kira’a) sun ce ma’anar “ba kai suke karyatawa ba” ita ce: su kansu kafiran ba su fadar cewa kai (ya Rasulallah) mai karya ne. Alhamdulillah, hatta Turawa da ake ganin suna da ilimi ba su fadar cewa Manzon Allah (SAW) mai karya ne duk da irin dabi’arsu ta yin abu keke-da-keke (su ga komai a sarari). Kila kuma aka ce ma’anar “ba kai suke karyatawa ba” ita ce: ba su da ikon kafa wata hujja da za su karyata Manzon Allah (SAW).
Kafiran sun san Manzon Allah (SAW) maigaskiya ne, wasu sun karyata shi ne saboda hassadar ba a aiko Manzo daga cikin kabilarsu ba. Kamar Abu Jahali yana adawa ne da gidan Banu Hashim, a ce akwai Annabta a gidan Banu Hashim amma shi babu a gidansu. Ko kuma Larabawan Bani Hanifa da suke bin Musailamtul Kazzab suna cewa “makaryacin Bani Hanifa ya fi mana mai gaskiyar Kuraishawa”, haka suke fada wa Sahabban Manzon Allah (SAW). Suna nufin Musailama makaryaci shi ne suke bi duk da gaskiyar Annabi (SAW).
Yana daga girmama Manzon Allah (SAW), Allah ya yi magana da Annabawa dukkansu da sunayensu, yana jan sunayensu karara, amma shi Manzon Allah (SAW) Allah bai kama sunansa ya kira ba sai dai ya yi masa alkunya. Misali, Allah ya ce “Ya Adamu”, “Ya Nuhu”, “Ya Ibrahimu”, “Ya Musa”, “Ya Dawudu”, “Ya Isah”, “Ya Zakariyya’u”, “Ya Yahya”, amma Allah bai kira Manzon Allah (SAW) da sunansa karara ba sai da kinaya. Wato “Ya ayyuhar Rasuulu”, “Ya ayyuhan Nabiyyu”, “Ya ayyuhal Muzzammil” ko “Ya ayyuhal Muddassir”. Wannan duk girmamawa ne ga Annabi (SAW).
Allah Ya Rantse Da Darajar Manzon Allah (SAW)
Duk abin da Allah (SWT) ya fada gaskiya ne kuma abu ne mai girma da ya fi gaban a misalta darajarsa, to ina ga kuma abin da ya yi rantsuwa a kansa?
A cikin Alkur’ani maigirma Allah (SWT) ya ce “Na rantse da rayuwarka su (mutanen nan) suna cikin dimuwa cikin kai da kawowarsu”. A cikin ayar nan Allah yana ba da labari ne a kan mutanen Annabi Ludu (AS) kan yadda suka yi nisa cikin abubuwan da suke aikatawa da aka hane su har ya kai su ga yin maye a ciki tare da kangare wa wa’azin da Annabi Ludu (AS) yake musu. Shi ne a cikin ba da labarin nasu Allah ya rantse da rayuwar Manzon Allah (SAW).
Malaman Tafsiri duk sun yi ittifaki cikin fassarar ayar cewa wannan rantsuwa ce daga Allah wanda ya yi da zamanin rayuwar Manzon Allah. Ma’anar rantsuwar tana nufin Allah (SAW) ya rantse da wanzuwar Manzon Allah (SAW). Kila kuma aka ce rantsuwa ce da rayuwarsa. Wanna karshen girmamawa ne a ce Allah ya rantse da rayuwarsa (SAW), karshen alheri ne da daukaka ga Manzon Allah (SAW). Sayyidina Abdullahi bin Abbas (RA) ya ce “Allah bai yi wata halitta mafi girma ba ga Manzon Allah (SAW). Ban taba jin Allah ya yi rantsuwa da rayuwar wani koma bayan sa (Ma’aiki) ba (SAW)”. Malam Abul Jauza’i (Mutumin Busra) ya ce “Allah bai taba rantsewa da rayuwar wani mutum ba in ba Annabi Muhammadu (SAW) ba, domin shi Annabi Muhammadu shi ne mafi girman halitta (talikai) duka a wurin Allah”.
Yana daga cikin rantsuwa da Manzon Allah (SAW) wata aya a cikin suratu Yaasiyn. Kafiran Makka sun ce wa Manzon Allah (SAW) “kai ba Ma’aikin Allah ba ne”, wannan Kalmar ba Annabi Muhammadu (SAW) shi kadai aka taba fada wa ba, duk Annabawan Allah (AS) an fada musu haka. Amma duk Annabin da kafiransa suka fada masa haka sai Allah ya kyale su; a bar Annabin da kansa ya rika ba su amsar cewa “wallahi ni Ma’aikin Allah ne”, amma a janibin Annabi Muhammadu (SAW) Allah ne yake amsa musu. Da suka ce shi ba Ma’aikin Allah ba ne, shi ne a farkon Suratu Yaasiyn Allah Ta’ala ya ce “Na rantse da Alkur’ani mai hikima (da aka kyautata shi). Kai kana daga cikin Manzannin Allah”.
Malaman Tafsiri sun yi sabani cikin ma’anar ayar farkon surar wato kalmar “Yaasiyn”. Malam Abu Muhammadul Makiyy (Mutumin Makka) ya ce an ruwaito daga Manzon Allah (SAW) ya ce “Ni ina da sunaye goma a wurin Ubangijina”, ya fada daga cikin sunayen akwai: “Daha, da Yaasiyn”. Idan an yi la’kari da ma’anar wannan, fassarar Yaasiyn za ta zama mai ma’anar ‘Ya Annabi Muhammadu’, sannan maganar rantsuwar ta biyo baya. Malam Abdulrahmanus Sulamiyy ya yi hikaya daga Sayyidina Imamu Ja’afarus Sadiki (daya daga cikin manyan Malamai daga Iyalan Gidan Manzon Allah SAW) cewa ma’anar Yaasiyn tana nufin ‘Ya kai Shugaba’. Wannan ma’ana tana da dadi, domin akwai wasu ‘yan’uwa da suke ganin ba za a kira Manzon Allah (SAW) da ‘Shugaba’ ba saboda tutiyar da suke yi da wata ruwayar da aka ruwaito yana fadar sunansa bai ce shi shugaba ba ne. To amma ya kamata a fahimci cewa domin Manzon Allah (SAW) ya fadi sunansa ba tare da ya sanya ‘shugaba’ ba a ciki ladabi ne kuma ya koyar da mu haka. Annabi Yahya da bai kai Annabi Muhmmadu (SAW) ba Allah ya ce masa ‘shugaba’ a cikin Suratu Ali Imran. Muma muna koyi da irin wannan ladabin, idan mutum ya je gidan wasu sai ya kwankwasa kofa aka tambaya waye? Ba zai ce ni ne Alhaji wane ko Malam wane ba, sai dai ya fadi sunansa, to su masu gidan ne za su ce ‘ah; Malam wane ko Alhaji wane’. Wannan koyi ne da irin ladabin Manzon Allah (SAW). Shi ya sa Imamu Ja’afarus Sadik ya ce ma’anar Yaasiyn tana nufin ‘Ya Shugaba’.