Farashin kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen ƙetare za su ƙara tsada, sabida yadda babban bankin CBN ya mayar da canjin Dala N951.941 zuwa N1,356.883 kan kowacce Dala ɗaya.
LEADERSHIP ta rawaito cewa masana tattalin arziki sun ce ko an daidaita yanayin tashin dala, to tsadar rayuwar da ake gani baza ta sauko nan take ba.
- Tsadar Magunguna Na Barazana Ga Rayukan Majinyata A Nijeriya
- Tsadar Rayuwa: ‘Yan Nijeriya Na Rungumar Bashin Banki
Idan za a iya tunawa dai, babban bankin CBN a ranar 24 ga watan Yuni 2023 ya daidaita farashin canjin Dala daga N422.30 zuwa N589 kan kowacce Dala ɗaya.
Haka ma a ranar 6 ga Yulin shekarar 2023, bankin ya daidaita canjin dalar zuwa N770.88 haka ma a a ranar 14 ga Nuwamba shekarar da ta shuɗe canjin ya kasance a haka.
A watan Disambar bara babban bankin ya daidaita canjin kan N783.17 da kuma N951.941 kan kowacce dala sai kuma a halin yanzu da bankin ya maida canjin N1,356.883 kan kowacce Dala ɗaya.