Hukumar da ke shirya gasar cin kofin kasashen Afirika na AFCON (CAF) ta bayyana adadin makudan kudaden da kasar da ta lashe kofin AFCON na bana zata samu.
- AFCON 2023:Mai Tsaron Ragar Nijeriya Nwabali Ya Murmure Daga Raunin Da Ya Samu
- AFCON 2023: Hasashe Ya Nuna Nijeriya Ce Za Ta Lashe Gasar Cin Kofin Afirika Ta Bana
CAF ta bayyana cewar duk kasar da ta yi nasara a gasar AFCON ta 2023 za ta samu makudan kudi har dala miliyan 7,yayinda kasar da tazo a matsayi na biyu zata karbi dala miliyan 4.
Haka kuma kasashen da suka buga matakin na kusa da na karshe kowace zata samu dala miliyan 2.5.
Kasashen da suka kai wasan daf da na kusa da na karshe, za a ba su dala miliyan 1.3,wadanda kuma suka fice a zagaye na 16 za a baiwa kowace kasa dala 800,000.
A matakin rukuni kuma wadanda suka kare a matsayi na uku zasu samu dala 700,000 yayinda na uku da na hudu a matakin rukuni kowanensu zai samu dala 500,000.