Jimillar kayayyakin soja da kasar Amurka ta sayar wa kasashen waje a shekarar kasafin kudi ta 2023 ta karu da kashi 16 bisa dari sama da na shekarar kasafin kudi ta 2022, inda ya kai dala biliyan 238. Wani binciken jin ra’ayin jama’a da CGTN ya gudanar ya nuna cewa, kashi 93.88 cikin dari na masu amsa tambayoyi a duniya sun yi Allah wadai da Amurka kan samun riba ta hanyar tada zaune tsaye da kuma rura wutar yaki a duniya.
A cikin binciken, kusan kashi 90 cikin 100 na masu amsa tambayoyi na duniya sun nuna damuwa cewa, Amurka na iya haifar da sabon zagaye na tserenya sayan makamai tsakanin kasashen duniya. Yayin da kashi 94.81 cikin dari na mutane suka yi imanin cewa, sayar da kayayyakin soja da Amurka ke yi ga kasashen waje yana da alaka da manufofinta na waje kuma ya zama abin riko mai mahimmanci ga Amurka wajen tilastawa da kuma sarrafa wasu kasashe. (Mai fassara: Yahaya)