Rundunar sojin Nijeriya da ke Jihar Katsina ta yi nasarar kubutar da mutane 35 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Tashar Nagulle cikin karamar hukumar Batsari.
Jami’an tsaron soji ne suka kubutar da mutanen daga maboyar ‘yan ta’addan, inda aka kashe da dama daga cikisu wasu kuma suka arce da raunuka.
- AFCON 2023: Saura Wasanni Biyu Nijeriya Ta Lashe Kofin Nahiyar Afirka
- Kakakin Majalisa Ga Tinubu: Ka Dauki Kwararan Matakai Kan Karuwar Matsalolin Tsaro
Da yake amsar mutanen da aka kubutar a sansanin soji na Batsari, shugaban karamar hukumar Alhaji Yusuf Mamman Ifo ya gode wa sojojin a kan wannan kokari.
Ya alakanta nasarar da kwazon gwamnatin Jihar Katsina da ta karamar hukumar wajen samar da tallafin da ake bukata.
Alhaji Mamman Ifo ya ce mutanen da aka kubutar za su ci gaba da zama a hannun karamar hukumar kuma za a samar masu tallafi kafin hada su da iyalansu.
Ya yi kira da a ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya mai dorewa a yankin da jiha da kasa baki daya.
Wasu mutum biyu daga cikin wadanda aka kubutar sun hada da Malama Hafsat Musa ta kauyen Nahuta da Tanimu Haruna daga Katsina sun bayyana irin ukubar da ‘yan ta’addan suka gana masu.
Sun gode wa sojojin a kan kubutar da su, inda kuma suka yi fatan suma sauran wadanda ke tsare da su a kubuta da su.