Kamfanin Rana Continental Synergy da hadin guiwar gwamnatin tarayya, sun karrama jihar Bauchi a matsayin gwarzowar jiha mai tasowa a bangaren mai da iskar gas ta shekarar 2024.
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ne ya amshi lambar yabon a madadin jihar, a yayin babban taron liyafa ta bangaren iskar gas da mai na Nijeriya da ya gudana a Abuja, wanda kuma kamfanin Rana Continental Syngergy ta shirya da hadin guiwar masu ruwa da tsaki a bangaren mai da iskar gas hadi da ma’aikatar albarkatun mai.
- Samar Da Jami’ar Musulunci A Jihar Kaduna Alheri Ne – Bola Ige
- Xi Ya Mika Gaisuwar Bikin Bazara Ga Dukkan Sinawa
Bala Muhammad wanda ya jinjina da kokarin masu shirya taron wajen zabar jihar gami da karramata, ya sha alwashin hada kai da shugaban kasa Bola Tinubu domin cimma manufar gwamnatin tarayya na shawo kan matsalolin da suka yi wa bangaren tattalin arzikin kasa dabaibayi.
Da ya ke samun wakilcin kwamishinan albarkatun kasa na jihar Bauchi, Hon. Muhammad Maiwada Bello, gwamnan ya misalta taron a matsayin mai cike da tarihi ta yadda jihar ta lashe kambon jiha mai tasowa a bangaren mai da iskar gas a 2024 a fadin kasar nan.
Ya ce, wannan nasarar da jihar ta samu bai rasa nasaba da tsare-tsare da kyawawan manufofin da suke akwai a bangaren mai da gas gami da saukaka harkokin kasuwanci musamman bayan gano Mai a kogin Kolmani da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar.
Ya ce, hakan zai kara janyo hankalin masu sha’awar zuba hannun jari domin su zo jihar su zuba hannun jarinsu domin cigaban jihar da ma kasa baki daya.
Maiwada Bello, ya ce, gwamnan jihar Bauchi na aiki tukuru domin kyautata bangaren makamashi domin tabbatar da samar da damarmakin zuba jari da ayyukan yi ga matasa.
Ya kuma ce, lambar yabon zai kara musu kumaji da kokarin zage damtse wajen yin duk mai yiyuwa domin kunkasa bangarorin makamashi.
A nasa jawabin, karamin minista (Gas) a ma’aikatar albarkatun mai, Ekperikpe Ekpo, ya ce, jihar Bauchi ta nuna kwarin guiwar za ta yi abun a zo a gani a bangaren makamashi yayin da take kokarin samar da damarmaki da kere-kere a bangaren masana’antun mai da gas a Nijeriya.
Da ya ke samun wakilcin daraktan gas na ma’aikatar Misis Oluremi Komolafe, ta ce, lambar yabon ya cancanci jihar Bauchi lura da rawar da take takawa wajen kyautata harkokin mai da iskar gas.