Wata kungiya mai zaman kanta, Women Voice and Leadership Project (WVL) ta wayar da kan masu ruwa da tsaki a kan aiwatar da dokar cin zarafin jinsi (GBV) a Kebbi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Global Affairs Canada ce ke daukar nauyin shirin na WVL da ActionAid Nijeriya ke gudanarwa.
- Auren Gata : Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Aurar Da Mata 300
- Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Nasir Idris A Matsayin Gwamnan Jihar Kebbi
Ya kuma bayar da rahoton cewa, wayar da kan jama’a ya kunshi taron tattaunawa kan aiwatar da dokar hana cin zarafin bil’adama (VAPP) a Kebbi.
Da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron tattaunawa da aka yi a Birnin Kebbi, Babbar Daraktar kungiyar ta Nana, Dakta Fatima Adamu ta ce sun hada kungiyoyi daban-daban na al’umma.
“Mun tattaro kungiyoyi daban-daban na al’umma kuma mun kira kanmu Collision of Community-based Organizations (CBOs) Against Henders Colence a Kebbi.
Dokta Fatima Adamu ta ce, “Babban makasudin haduwa don tattaunawar ita ce tattaunawa mai ma’ana a tsakanin masu ruwa da tsaki don aiwatar da dokar cin zarafin jinsi musammam irin yadda ake yiwa ‘ya’ya mata fyade da cin zarafi a gidajen aure ko a waje.
Ta kara da cewa tattaunawar ta kasance kan matakin aiwatarwa, nasarori da kalubalen da ake fuskanta wajen aiwatar da dokar VAPP a jihar Kebbi, inda ta ce tattaunawar ta hada jami’an gwamnati, kungiyoyin farar hula, masana shari’a da shugabannin al’umma.
A cewarta, da nufin samar da wani dandali ga masu ruwa da tsaki domin yin musayar ra’ayi, tattauna hanyoyin da suka dace da kuma magance kalubalen da ake fuskanta wajen aiwatar da dokar VAPP a jihar baki daya.
Shugabar ta tuna cewa kimanin shekaru biyu da suka gabata sun ba da shawarar kuma sun sami amincewa da Dokar VAPP, tana mai cewa: “amma mun lura cewa an yi shiru, mun gano inda muke da kalubalen da muke fuskanta don samar da mafita.
“Kawai masu ruwa da tsaki wadanda ke da rawar da za su taka wajen aiwatar da shirin da aka gayyata kuma duk mun amince cewa wannan mafari ne, wasu sun ba da shawarar a rika shirya shi duk shekara ko shekara biyu domin a nuna inda muke wajen aiwatar da shi. ” in ji ta.
Dangane da kalubalantar katsalandan a shari’ar VAPP da wasu manyan ‘yan siyasa da wasu masu hannu da shuni ke yi a cikin al’umma, Daraktar ta ce wasu daga cikin wadannan mutane sun kai ga baiwa jami’an shari’a da jami’an tsaro cin hanci don samun mafita ga shari’un fyade ko na cin zarafin jinsi.
Hakazalika ta koka da yadda wasu daga cikin irin wadannan mutane kan yi amfani da karfinsu wajen biyan iyayen wadanda suka tsira da ransu wajen lalata shari’ar, yayin da wasu ke yin tasiri ga umurnin da aka bayar na a lalata shari’ar a yayin da ta ke a gaban alkalai.
Duk da haka, Dakta Fatima Adamu ta ce sun fahimci cewa a cikin dokar, “akwai dokar kariya da ya kamata ta magance irin wannan yanayin amma ba mu yi amfani da shi ba. Don haka, yanzu muna da kalubalen don ganin yadda za mu iya jajircewa wajen amfani dokar, inji ta.”
Haka kuma ta kara da bayar da shawarar shigar da kafafen yada labarai a cikin shari’o’in da ke da karfin gaske da nufin yada lamarin don hana ci gaba da lalata shari’o’in a yayin da suke a gaban kotu daga manyan mutane da masu fada a ji.
Daga karshe ta ce ina sa ran kungiyar sa kai a karshen shirin gaba dayan shi, zasu jajirce wajen ganin an rage da hana yawan kararraki ta hanyar karya al’adar yin shiru da tsoma baki daga masu iko da masu arziki.