Shugaban kamfanin bunkasa albarkatun ma’adanai na Jihar Kaduna, Dakta Mohammed Nura Sani Hussaini ya bayyana cewa a duk fadin Nijeriya yankin Birnin Gwari mai fama da matsalar tsaro shi ne yankin da ya fi kowanne yanki yawan albarkatun ma’adanai sama da shekaru 100 da suka gabata.
Ya dai bayayana hakan ne a zantawarsa da wakilinmu, inda ya ce tuni gwamnatin Jihar Kaduna ta fara nemo masu saka hannun jari a bangaran domin bunkasa tattalin arzikin jihar baki daya.
- Minista Idris Ya Ƙaddamar Da Ƙungiyar Kakakin Labarai
- Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Sake Tsara Ayyukan Hakar Ma’adanai
Shugaban ya ce sama da shekaru 100 da suka gabata babu irin nau’in ma’adanan da babu a Birnin Gwari, amma rashin tsaro ya sanya aka bar su kara zube wanda yanzu suke kokarin farfado da su.
Ya ce yanzu gwamnatin Jihar Kaduna ta dukufa wajen daukar matakan tsaro a yankin domin samun daman hako ma’adanan, wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar al’umma baki dada.
Shugaban ya kara da cewa tuni manyan kamfanonin hakar ma’adanai suka nuna sha’awarsu na shigowa yankin domin fara hakar ma’adanai, wanda nan gaba kadan za a bude yankin domin fara aiki gadan-gadan.
Ya ce har yanzu gwamnatin Jihar Kaduna ba ta bayar da umurnin hakar ma’adanai a Birnin Gwari ba, yana mai cewa duk wanda yake aiki a yankin, to sojan gona ne.