Jam’iyyar PDP ta samu nasarar lashe zabe biyu a kan jam’iyyar APC da ta samu kujera 1 a zabukan da aka sake gudanarwa a rumfuna 46 a bisa ga hukuncin kotun daukaka kara.
Baturen zaben mazabar Tarayya ta Yabo/Shagari, Farfesa Abubakar Abdullahi Bagudo ya bayyana Umar Yusuf Yabo na jam’iyyar PDP da ke kan kujerar a matsayin wanda ya yi galaba da kuri’u 26, 829 ta hanyar kayar da dan takarar APC, Umar Abubakar da kuri’u 26, 113.
- PDP Ta Lashe Zabukan Cike Gurbi, Tsohon Kakakin Majalisar Bauchi Ya Dawo Majalisa
- AFCON 2023: Zamu Canza Salon Wasanmu Yayin Karawa Da Nijeriya-Â Kocin Afirika Ta Kudu
Haka ma Farfesa Farouk Tambuwal, baturen zaben mazabar Majalisar Dokoki ta Jiha a Bodinga ta Arewa ya bayyana Honarabul Abubakar Magaji na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya yi galaba a kan Yusuf Marafa Danchadi na APC da kuri’u 6, 488 da kuma 5, 893.
A zaben Majalisar Dokoki ta Jiha a mazabar Tambuwal ta Yamma kuwa, Farfesa Bayero Kasim Bukkuyum ya bayyana Bashir Ahmed na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya samu nasara da kuri’u 19, 315 yayin da Sulaiman Hantsi Romo na PDP da ke kan kujerar ya samu kuri’u 19, 021.
Tuni dai Jam’iyyar PDP a Jihar ta bayyana rashin amincewa da zaben Majalisar Dokoki a Tambuwal ta Yamma a bisa ga abin da ta kira kwacen akwati da canza sakamako a rumfar da PDP ta samu nasara wanda ya sabawa dokokin zabe kamar yadda Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya bayyana.
Zaben wanda ya samu fitowar jama’a sosai a rumfuna 46 da aka aiwatar da shi a Jihar, ya gudana ne da sayen kuri’u da tsada a tsakanin manyan jam’iyyun biyu duk kuwa da bayyanar jami’an Hukumomin yaki da cin hanci na EFCC da ICPC.